Yarinyar da ke rubutu da yatsun ƙafa ta sami damar shiga jami’a

0
330

Yarinyar nan ‘yar shekara 22 da haihuwa mai suna Maryam Umar wadda aka haifa ba tare da hannu ba, ta roki ‘yan Najeriya masu tausayi da gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su kawo mata agaji domin ta kammala rijistar ta zuwa Jami’ar Jihar Gombe.

Maryam ta samu gurbin karatu a fannin tattalin arziki kuma sai ta biya kuɗi makaranta N81,322.50.

Yarinyar da ke da ƙwarewa ta musamman wajen rubutu da yin ayyukan gida da yatsunta na ƙafa ta ce a shirye take ta fara karatu a jami’a.

Da take neman a taimaka mata a wata tattaunawa da ‘yan jarida a ɗakin taro na wakilan ‘yan jarida na jihar Gombe, Maryam ta ce iyayenta ba su da abin da za su ba ta damar ci gaba da karatunta, inda ta ce ta tsira ne da sadaka daga mazauna garin.

Ta ce, “Iyayena suna zaune a BCGA, Gombe, na kammala karatun sakandare a 2022. Na ci 182 a UTME kuma na riga na sami kredit hudu ciki har da Ingilishi da Lissafi a NECO.

KU KUMA KARANTA: Tirƙashi! Ƙani ya Ƙwace matar yayansa a Kenya

“Amma ba ni da kuɗin rajista don karantar tattalin arziki a Jami’ar Jihar Gombe. Iyayena ba su da kuɗi kuma ina kira ga masu kishin jama’a da su ba ni goyon baya don kada in ɓata wannan damar.”

Maryam ta bayyana cewa ta fito daga babban gida, inda ta ƙara da cewa mahaifinta yana da ‘ya’ya takwas. “ni ce ‘ya ta uku kuma ni kaɗai aka haifa ba tare da hannu ba.

“Ina so in yi kasuwanci idan na kammala karatuna, ”in ji ta.

Ta ci gaba da cewa ta zaɓi ta ga iya iyawa a cikin nakasar ta, ta lura cewa a zahiri ta yi wa kanta komai ba tare da ta ɗora wa kowa alhakinta ba.

Maryam ta ce, “Na ji daɗi da na ga iyawa a cikin naƙasata kuma duk abin da koya za a iya yi da hannu zan iya yi da ƙafa.”

Masu son su taimaka mata za su iya ba da gudummawa ga asusun bankin Maryam Umar na bankin Union Bank: 0015749904.

Leave a Reply