Yarima Salman na Saudiyya, ya jaddada goyon bayan Saudiyya ga al’ummar Falasɗinawa

0
217

Daga Ibraheem El-Tafseer

Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed Bin Salman ya tattauna da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ta wayar tarho.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya ba da rahoton cewa, Yarima Bin Salman ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da “taimaka wa al’ummar Falasɗin don cimma halastaccen ‘yancinsu na rayuwa mai kyau, da cimma buri da fatansu da kuma samun zaman lafiya mai ɗorewa.”

Ya kuma shaida wa Shugaba Abbas cewa yana aiki tare da dukkan ɓangarorin ƙasashe da na shiyya-shiyya don hana “ƙazancewar” rikicin.

Ya kamata a tuna cewa Abbas da Hamas mai iko da Zirin Gaza, abokan hamayya ne na siyasa.

Abbas ne ke jagorantar ƙungiyar Fatah mai iko da gaɓar yamma da kogin Jordan. Shi ne kuma shugaban ƙungiyar tabbatar da ‘yancin Falasɗinu (PLO).

KU KUMA KARANTA: Hamas ta kai harin bazata a Isra’ila, ta kashe mutane 200, wasu 779 sun sami raunuka

Sai dai goyon bayan Saudiyya ga Falasɗinawa na da matuƙar muhimmanci, domin ya saɓawa koma-bayan tattaunawar ɓangarori guda uku da aka yi tsakanin Isra’ila da Saudiyya, da kuma Amurka da nufin daidaita alaƙa tsakanin gwamnatin Riyadh da ta Tel Aviv.

Manazarta na ganin cewa rikicin da ya ɓarke ya haifar da mummunar illa ga tattaunawar daidaita tsakanin manyan ƙasashen biyu na Gabas ta Tsakiya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar bayan harin Hamas, Saudiyya ta ɗorawa Isra’ila alhakin taɓarɓarewar lamarin.

Leave a Reply