Yara Falasɗinawa da dama a birnin Gaza da ke arewacin yankin Gaza sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ƙarancin abinci da ruwan sha a ƙarƙashin mamayar da Isra’ila ke yi.
Yaran sun yi tattaki ne a ranar Talata a titunan birnin Gaza riƙe da tutoci ɗauke da rubuce-rubucen “burudi ne mafarkina a kullum” da kuma “muna son abinci,” da dai sauransu.
Riƙe tukwanen da babu komai a ciki a lokacin gangamin nuna rashin abincin, yaran sun yi ta ihun neman rayuwa mai kyau.
“Muna mutuwa da yunwa, ba mu da abin da za mu ci, ana tilasta mana cin abincin dabbobi,” Ayat Ashour ‘yar shekara 10 ta shaida wa Anadolu.
Ta ƙara da cewa “Ba ma iya samun abinci, muna so mu rayu, muna son agajin abinci. … Mutanen arewacin Gaza ba sa samun abin da za su ci, babu madara ga yara,” in ji ta.
KU KUMA KARANTA: Fiye da kashi 95 na al’ummar Sudan ba sa iya samun abinci sau ɗaya a rana – WFP
Wani yaro Omar al Shenbari, mai shekara 14, ya ce: “Muna tafiya ne domin mu ɗaga muryarmu ga duniya cewa muna son mu ci burodi, babu abinci ko ruwa (a Gaza).”
“Sau ɗaya muke cin abinci a rana kuma shi ma ba ya ƙosar da mu, galibi ruwa ne da tumatir,” in ji Omar.
A ƙarshe ya aike da saƙo zuwa ga duniya yana mai cewa: “Muna cikin mawuyacin hali, dole ne ƙasashen Larabawa da ma duniya baki ɗaya su tsaya tare da mu.”