‘Yar Ganduje ta shiga cikin badaƙalar saki

2
605

A ranar Alhamis ne Alkalin kotun shari’ar musulunci a jihar Kano, mai shari’a Abdullahi Halliru, a jiya a Kano ya kori ‘yan jarida da suka taru a kotunsa domin sauraren ƙarar sakin ɗiyar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje wadda ta kai mijinta kotun inda ta nemi a gaggauta sakin ta.

‘Yar gwamnan mai suna Asiya Balaraba, ta shigar da ƙara a gaban kotun domin neman a raba aurenta da mijinta Inuwa Uba, bisa dalilin cewa ta daina jin daɗin auren, haka kuma mijin ya yi anfani da muƙaminsa,ya damfare ta, tare da karkatar da dukiyarta da kuɗinta dan amfanin kansa.

Mai shari’a a wannan lokaci ya shaida wa ‘yan jarida cewa matar da ake magana a kan neman a raba aurenta ‘yar Gwamnan Jihar Kano ce a yanzu, ya kamata a kula da shari’arta da gata ta musamman, don haka ya umarci manema labarai da sauran masu sha’awar jin labarin, da suka je kotu domin su bar zauren kotun.

KU KUMA KARANTA:Lauya ya yi wa tsohon mijin wacce yake karewa duka a kotu

Alƙalin ya zaɓi ya saurari ƙarar a zaurensa, tare da rokon cewa duk da cewa dukkan ‘yan Najeriya daidai suke, amma akwai shari’o’in da ba su da buƙatar a rika yaɗawa domin kuwa wannan lamari na ɗaya daga cikin abubuwan da ya damu da shi, don a ƙarshe, ma’auratan za su iya sasantawa.

Yayin da tuni aka yi ta yaɗawa jama’a, auren yana da shekara 16, Asiya Balarabe, ta roƙi kotu ta yi amfani da tsarin shari’a ta raba auren.

A kwanakin baya ne dai wata majiya mai tushe daga ‘yar gwamnan ta bayyana cewa, wasu jami’an tsaro sun je gidan ma’auratan da ke Kano, inda suka shiga gidansu da ke technical staff quarters tare da kwashe wasu muhimman takardu na ma’auratan, duk da cewa ana zargin akwai na cikin gida.

Ana kuma zargin Alhaji Inuwa Uba da mayar da kamfanin shinkafar su da ke kan titin Kano zuwa Zaria, da kuma wajan taron biki da wani gida a Abuja da gidajen man su, da dai sauransu zuwa kadarorinsa, amma duk da haka alƙali ya ba su shawarar su koma gida nan da makonni biyu su sasanta bambance-bambancen da ke tsakaninsu ko kuma su dawowa don cigaba da sauraron ƙarar.

2 COMMENTS

Leave a Reply