‘Yansandan a ƙasar Finland sun kama mai fafutukar kafa ƙasar Biyafara, Simon Ekpa

0
19
‘Yansandan a ƙasar Finland sun kama mai fafutukar kafa ƙasar Biyafara, Simon Ekpa

‘Yansandan a ƙasar Finland sun kama mai fafutukar kafa ƙasar Biyafara, Simon Ekpa

Hukumomin ƙasar Finland sun kama mai fafutukar kafa ƙasar Biafra, Simon Ekpa, a bisa tuhume-tuhumen aikata ta’addanci.

Hukumar binciken ƙasar Finland ta ce ta buƙaci a tsare Ekpa a kan zargin tunzura jama’a su aikata laifi, kuma suka aikata hakan da niyyar ta’addanci.

Ana tuhumar Ekpa ne tare da wasu mutanen 4 da zargin ɗaukar nauyin laifuffukan ta’addanci, a cewar sanarwar da ‘yan sandan ƙasar Finland suka fitar a ranar Alhamis.

Duk da cewa sanarwar ‘yan sandan bata ambata sunan Ekpa ba, shafin yanar gizon wata kafar yada labaran kasar Finland, Helsingin Sonamat, ya zayyano sunansa a rahoton daya wallafa game da batun.

KU KUMA KARANTA:Rundunar tsaron Najeriya ta yaba da cafke Simon Ekpa

Sanarwar ‘yan sandan ta bayyana cewa “bukatar tsarewar nada nasaba da wani binciken aikata laifffuka inda ake zargin wani dan Najeriya mai shaidar zama dan Finland da aka haifa a shekarun 1980 ta tunzura jama’a su aikata laifi, kuma suka aikata hakan da niyar ta’addanci.

A watan Maris da ya gabata ne shelkwatar tsaron Najeriya ta ayyana neman daya daga cikin shugabannin haramtacciyar kungiyar ‘yan awaren Biafra, Simon Ekpa, ruwa a jallo.

An wallafa sunan Simon Ekpa a jerin sunayen mutanen da hukumomin sojan Najeriya ke nema tare da wasu mutum 96 suka fito daga sassan kasar daban-daban.

A jikin wani kwali me dauke da hotunan mutanen da ake tuhuma, shelkwatar tsaron tace ta ayyana sunayen mutane 97 da take nema ruwa a jallo saboda laifuffukan ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da barazanar ballewa daga najeriya.

Leave a Reply