‘Yansanda sun kama wani ɗan Nijar da ake zargi da safarar makamai
Rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta kama wani tsoho ɗan Jamhuriyar Nijar mai shekaru 58 da haihuwa da ake zargi da safarar makamai daga ƙasar Aljeriya zuwa Najeriya tare da ƙwato bindigogi ƙirar AK47 guda 16.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Zamfara, CP Shehu Mohammad Dalijan wanda ya gabatar da waɗanda ake zargi da aikata laifuffaka daban daban su 22 a hedikwatar ‘yansanda, da ke Gusau a jiya Talata ya ce waɗanda ake zargin sun haɗa da wani mai ƙera bindigogi ƙirar AK 47 da kuma bindigogi ƙirar SMG wanda aka kamo daga jihar Filato.
Kwamishinan ‘yansandan ya ce rundunar ta kuma kama wasu da ake zargi da suka hada da masu samar da kayan aiki ga ‘yan bindiga wadanda aka kama su da tsabar kuɗi naira miliyan biyu da dubu ɗari biyar a lokacin da suke hanyar zuwa kasuwa domin sayawa yan bindiga babur.
Ya ƙara da cewa sun kuma kama harsashai, da tabar wiwi da layoyi da sihiri daga hannun waɗanda aka kama.
A cewarsa, sauran waɗanda aka kama sun haɗa da masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, tare da ƙwato na’urorin haƙar ma’adinai.
KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda sun kama ‘yan ƙasar waje 113, da ake zargi da sata ta yanar gizo
Dalijan ya bayyana cewa ‘yansanda sun samu nasarar kama su a wasu sassan jihar Zamfara, Filato da Sokoto.
Ya ce sun yi aiki ne da sahihan bayanai da suka samu don cimma nasarar tare da yin kira ga mazauna yankin da su tallafawa hukumomin tsaro da muhimman bayanai.
Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa gwamnatin tarayya da na jihar sun haramta hakar ma’adanai a fadin jihar don haka ya yi ƙira ga duk masu aikata wannan aika-aikar da su dakatar da yin hakan.