‘Yansanda sun kama Muhyi Magaji, shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Wata tawagar ‘yansanda ta musamman ta Sufeto Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, a safiyar Juma’ar da ta gabata, sun kama Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado.
Jaridar Solacebase, ta rawaito cewa, karkashin jagorancin ASP Ahmed Bello, sun mamaye ofishin hukumar, suna mai cewa sun samu umarni don su tafi da Muhuyi Rimingado.
Rahotanni sun bayyana cewa an tafi da shi zuwa hedkwatar ƴansanda ta shiyya ta daya a Kano, inda a bisa wani umarni daga sama aka hana shi ganawa da lauyoyinsa.
Binciken Solacebase ya nuna cewa wannan lamarin ya shafi karbe kadarori da ake zargin suna da alaka da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
KU KUMA KARANTA:‘Yansanda sun fake da barazanar tsaro ne kawai don su hana Maulidin Tijjaniyya – Gwamnatin Kano
Bugu da ƙari, bincike ya nuna cewa sabanin ya shafi shari’ar tsohon Manajan Daraktan Hukumar Samar da Kayayyakin Noma ta Jihar Kano (KASCO), Bala Muhammed Inuwa, wanda ake tuhuma da karkatar da kudaden gwamnati har na sama da Naira biliyan hudu (N4bn).
Sai dai wata majiya ta tabbatar da cewar Barr Muhuyi ya shaki iskar yanci cikin daren juma’a da misalin karfe 10:30 na dare jami’an Yan sandan sun sake shi.
“Inda Muhuyi ya tabbatar da cewar tsohon Gwamnan Kano kuma Shugaban Jami’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ne yasa aka kamashi,
Sakamakon kwace wasu kadarori nashi, inda yace idan har shine akan kujerar shugabar karbe korafe-korafe da hana ci da rashawa a Kano zai cigaba da gudanar da ayyukanka babu sanni babu sabo”