‘Yansanda sun kama malamin kwalejin da ya yi fyaɗe a ɗalibai huɗu a Yobe

0
177

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta kama Malam Adamu Garba Hudu, malami a kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta Al-Ma’arif da ke Potiskum, makaranta ce mai zaman kanta da ke ƙaramar hukumar Potiskum a jihar Yobe bisa zargin aikata laifin fyaɗe.

Malamin da aka kama ma’aikaci ne a Asibitin ƙwararru na jihar Yobe da ke Potiskum, kuma malami ne (visiting lecturer) a makarantar Al-Ma’arif, makarantar jinya mai zaman kanta da ke Potiskum, inda waɗanda abin ya shafa suke makaranta.

A binciken da Neptune Hausa ta yi, ta binciko cewa wanda ake zargin malami ne da ke koyar da ilimin taɓin hankali (mental health psychiatric Nursing) a makarantar, an kama shi ne bayan da ake zarginsa da yi wa ɗaya daga cikin ɗalibansa fyaɗe da kuma yadda yake riƙa jan ɗalibansa domin yin lalata dasu don ya ba su maki.

KI KUMA KARANTA: Ana yi wa yara fyaɗe sakamakon yaƙin da ke faruwa a Sudan – MƊD

An kama malamin da ake zargin ne bayan ya yi wa wata ɗaliba fyaɗe a ofishinsa da ke Asibitin ƙwararru na Potiskum.

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem, ya ce ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin ne a ranar Talata bisa zargin ‘Fyaɗe, cin zarafi da cin amana kuma ana ci gaba da bincike’.

DSP Dungus ya ce an kama malamin ne bisa zargin lalata da kuma yi wa ɗalibai fyaɗe a makarantar da yake koyarwa da kuma ofishinsa da ke Asibitin ƙwararru na Potiskum.

Ya ƙara da cewa aƙalla ɗalibai huɗu ne a makarantar waɗanda ya yi lalata da su inda ya ce wanda ake zargin yana da sha’awar lalata da ɗalibansa don ya ba su maki.

“Wanda ake zargin yana hannunmu. An kama shi ne a ranar Talata bisa zargin fyaɗe, cin zarafi da kuma cin amana. Ana ci gaba da gudanar da bincike,” in ji kakakin na ‘yan sandan jihar Yobe.

Leave a Reply