‘Yansanda sun kama gungun riƙaƙƙun ‘yan fashi da makami a Katsina

0
18
'Yansanda sun kama gungun riƙaƙƙun ‘yan fashi da makami a Katsina

‘Yansanda sun kama gungun riƙaƙƙun ‘yan fashi da makami a Katsina

Waɗanda aka kaman sun haɗa da, wani gungun ɓata-gari mai mambobi 7 da ake zargin ‘yan fashi da makamin da suka tare matafiyan dake safarar atamfofi da yaduddukan da aka ƙiyasta kuɗinsu zai kai Naira miliyan 4.

Rundunar ‘yansandan Katsina ta kama aƙalla ɓata-gari 15 da take zargi da aikata laifuffuka daban-daban a jihar.

Sanarwar da kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq ya fitar a yau Juma’a tace, an kama gungun ‘yan fashin ne a ranar 8 ga watan Satumbar da muke ciki, da misalin karfe 2 na rana, lokacin da jami’an ‘yan sanda daga yankin Funtua suka kai samame a bisa samun bayanan sirri.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun kashe mutane 5 a iyakar Nijar da Najeriya

Ya kara da cewa an yi nasarar kwato banduran atamfa 94 da leshi-leshi da bandura 2 na yadudduka, da aka kiyasta kudinsu zai kai naira miliyan 4 yayin samamen.

Har ila yau, rundunar ta cafke wasu mutane 3 da take zargi da mallakar bindiga kirar gida, a matsayin wani bangare na matakan da take dauka na karfafa aniyarta ta magance laifuffuka da tabbatar da zaman lafiyar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here