‘Yansanda a Zariya, sun kama matashi ɗan ƙabilar Ibo da zargin fyaɗe

0
6
'Yansanda a Zariya, sun kama matashi ɗan ƙabilar Ibo da zargin fyaɗe

‘Yansanda a Zariya, sun kama matashi ɗan ƙabilar Ibo da zargin fyaɗe

Daga Idris Umar, Zariya

A ranar Litinin da ya gabata ne hukumar ‘yansandan Najeriya reshen kasuwar Mata dake ƙaramar hukumar Sabon Garin Zariya jihar Kaduna suka yi nasarar kama wani matashin ɗan ƙabilar Ibo da zargin yiwa wasu ƙananan yara guda biyu fyaɗe.

Matashin mai suna Oguchuwku ya shiga komar ‘yansandan ne lokacin da asirinsa ya tonu.

Wakilinmu ya ziyarci ofishin ‘yansandan na kasuwar Mata, inda DPO ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace suna bincike kafin su tura gaban Kwamishina ‘yansandan jihar don ci gaba da bincike.

Bincike ya nuna cewa duka yaran biyu an kai su asibiti don gudanar da gwaji .

Hajiya A’ishatu Ahmed itace shugaban cibiyar Salama Centre dake Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya.

Hajiyar ta tabbatar da kawo yaran cibiyar tasu kuma ta shaida wa manema labarai bincikensu ya tabbatar da cewa anyi amfani da yaran amma sun ɗora yaran akan magani.

KU KUMA KARANTA:An kuɓutar da mata 9 masu ciki daga wata maƙyanƙyasar jarirai a Abuja

Shugaban ta kara cewa tuni sun tura sakamakon ga ofishin jin kai da walwala ta jihar Kaduna don ci gaba da bincike da daukar mataki kamar yadda suka saba.

Shima shugan kungiyar ciyamomin jihar Kaduna (ALGON) Hon Jamilu Abubakar Albani ya nuna takaicinsa a lokacin da yaji labarin faruwar lamarin .

Yayin da yake zantawa da wakilinmu ta wayar salula ya nuna damuwa matuƙa.

Shugaban yace, tabbas baza su zura ido akan irin wannan mugun ɗabi’a ba dole ayi kwakwalwaran bincike akan lamarin tare da yin adalci.

Shugaban ya ziyarci ofishin yan’sandan na kasuwar mata cikin hanzari don binciken lamarin wanda hakan ya sanya ana bibiyar lamarin sosai bangaren ƙaramar hukumar da kungiyoyin ƙare haskin Bil’adama da ƙafafen watsa labarai.

Ya zuwa haɗa wannan rahoton an tabbatar da cewa yaran yan makaranta Jafaru Firamare School ne

Kuma bubbar daga cikinsu tana da shekaru 10 ƙaramar tana da shekaru 9

Munso jin ta bakin kakakin hukumar yan’sandan na jihar Kaduna amma lamarin ya cutura

Leave a Reply