‘Yansanda a Zamfara sun cafke mutane 4 da harsasai 441

0
33
'Yansanda a Zamfara sun cafke mutane 4 da harsasai 441

‘Yansanda a Zamfara sun cafke mutane 4 da harsasai 441

Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen ƙaramar hukumar Anka ta samu nasarar cafke wasu ma’aurata da ake zargin ‘yan bindiga ne ko kuma suna da alaka da ‘yan bindigar da kuma wasu mutane biyu ɗauke da harsasai 441 da aka yi niyyar kai wa ‘yan bindiga a yankin.

Waɗanda ake zargin su ne Mamuda Makakari da matarsa Kuluwa Mamuda Wanda ke goye da ƙaramar yarinya tare da wasu ‘yan mata biyu, Maryam Sani da Amina Jijji, a sa’adda suke kan hanyarsu ta zuwa sansanin ‘yan bindiga a dajin Makakari.

Rahotannin sun bayyana cewa waɗanda ake zargin su na hanyar su ta kai wa wani dan bindiga da ke cikin dajin na Mamakari harsasan bindiga ne lokacin da aka kama su.

Karamar Hukumar Anka dai ta kasance wani wuri da ‘yan fashi ke yawan kai hare-hare akai akai, sannan yankin ya yi ƙaurin sunan tara yawan dabobin ‘yan bindiga ciki har da dabar wadanda ke da alaƙa da Kachalla Halilu Sububu kasurgumin dan bindigar da aka kashe a kwanan nan.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Borno sun kama 1 daga cikin fursunonin da suka tsere

Hakazalika, akwai wuraren haƙar ma’adanai mallakin ‘yan bindigar a yankin.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa daga Gusau aka aike da lambar wayar dan aiken da kuma ta wanda zai amshi sakon, lamarin da ya nuna cewa suna shiga tsakani a harkar cinikin makamai.

Yanzu haka dai hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike amma ba su kai ga fitar da wani bayani ba a hukumance ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here