‘Yansanda a Zamfara, sun cafke matan shugabannin ɓarayin daji ɗauke da makamai

0
60
'Yansanda a Zamfara, sun cafke matan shugabannin ɓarayin daji ɗauke da makamai

‘Yansanda a Zamfara, sun cafke matan shugabannin ɓarayin daji ɗauke da makamai

‘Yan sandan jihar Zamfara sun yi faretin wani Jam’in Civil Defense da ke yi wa ‘yan bindiga safarar makamai, Likitan jabu, da matan manyan ‘yan bindiga cikin wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta yi faretin, wasu mutane da ake zargi da hannu wajen kai wa ‘yan bindiga alburusai, da safarar miyagun kwayoyi, da sauran manyan laifuka.

Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a shalkwatar ‘yan sandan a Gusau, Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar, Shehu Muhammad Dalijan, ya ce, wannan kamen da suka yi, na zaman wani bangare ne na kokarin maido da zaman lafiya a jihar da kuma magance matsalar tashe- tashen hankula da ake fama da su a jihar.

Daga cikin wadanda ‘yan sandan suka kama, akwai wani jami’in hukumar tabbatar da kare lafiya da dukiyoyin al’umma na NSCDC wanda aka fi sani da Civil Defense, ASC 2 Maikano S/Tasha.

An same shi dauke da alburusai masu yawa da suka hada da harsashin bindiga samfirin AK-47 da harsashin bindigar harbo jiragen sama, sannan kuma an same shi da miyagun kwayoyin da suka hada da tabar wiwi da wasu nau’ukan kwayoyi.

Maikano, wanda ya amsa tuhumar da ake masa akan rawar da ya taka ga marawa ayyukan ‘yan bindigar baya, ya yi ikirarin cewa, wannan shi ne karon farko da ya yi wa ‘yan bindigar safarar makamai.

KU KUMA KARANTA:’Yansanda 5 sun rasu a wani hatsarin mota

Ya ce “E an kama ni da kwayoyi da harsashe wanda nake nufin kaiwa sansanin ‘yan fashi, amma wannan shi ne karo na farko.”

Maikano ya kuma kara da cewa ya yi zargin wani jami’in hukumar ta Civil Defense, ASC 2 Aminu Musa, wanda ya ce shi ne ya yake ba shi wadannan haramtattun kayayyaki ya yi wa ‘yan bindiga safarar su wanda ake amfani da su a kashe al’umma a jihar.

‘Yan sandan sun kuma gabatar da wani likitan boge, mai suna Mamuda Sani Makakari, wanda suka kama shi da harsashe har 441 a garin Anka.

Makakari, wanda shekaru biyu da suka gabata an kama shi da aikata irin wannan laifin, ya yi wa ‘yan sandan bayani cewa shi ne mai duba lafiyar ‘yan bindigar da iyalansu saboda a cewar shi, sai da magani ne sana’ar shi.

Ya kuma shaida cewa shi ba kwararen likita ko jami’in lafiya ba ne.

“Ina sayar da magani ne a kauye da unguwanni, cikin kwastamomi na har da su ‘yan fashin,”in ji shi.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma damke matan wasu mashahuran shugabannin ‘yan bindigar da suka hada da matar Kachalla Jijji da matar Bello Kaura kuma an kama dukkanin matan da’ ya’yansu hudu, kuma ana zarginsu da taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ayyukan da mazajensu ke yi.

Bayan wadannan muggan irin, an kuma yi faretin wani matashi mai suna Ashiru Hadi daga garin Kurar Mota, wanda ake zargi da kashe kakarsa.

Leave a Reply