‘Yansanda a Kebbi sun tabbatar da kashe Basaraken da aka yi garkuwa da shi

0
83
'Yansanda a Kebbi sun tabbatar da kashe Basaraken da aka yi garkuwa da shi

‘Yansanda a Kebbi sun tabbatar da kashe Basaraken da aka yi garkuwa da shi

Daga Idris Umar, Zariya

Rahotanni sun tabbatar da kashe Basarake a jihar Kebbi mai suna Alhaji Isah Daya, uban ƙasar Kanya da wasu mutane Takwas da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar.

Neptune Prime Hausa ta rawaito cewa an yi garkuwa da Basaraken ne tare da mutane takwas a gundumar Kanya ta ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a ranar 6 ga watan Oktoba.

Tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yansanda, sojoji, da ‘yan banga, sun yi nasarar ceto takwas daga cikin waɗanda aka sace a cikin dajin Sakaba a ranar Talata da karfe 10:00 na safe. Haka kuma waɗanda aka ceto an garzaya da su a babban Asibitin Sakaba don duba lafiyar su.

KU KUMA KARANTA: Yan bindiga a Kebbi sun kashe mutum 1, sun sace Basarake

Sai dai abin takaicin shi ne, an gano gawar basaraken gundumar ta Kanya a lokacin da ake aikin ceto su a cikin dajin Sakaba.

Kwamishinan ‘yansanda CP Bello Muhammad Sani ya miƙa ta’aziyya ga gwamnatin jihar da masarautar Zuru da iyalan marigayin, inda ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa.

Rundunar ‘yansandan ta bukaci jama’a da su bayar da bayanan da suka dace don taimakawa wajen kamo wadanda suka aikata laifin.

Duk mai bayani zai iya tuntuɓar hukuma don tallafawa binciken don samun nasarar aikin da ake yi.

Leave a Reply