‘Yansanda a Kano sun fitar da sabbin matakan tsaro a watan Azumi
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Kakakin yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar ta samar da tsare-tsaren na tsaro domin tabbatar da ganin an gudanar da azumin lafiya.
Sabbin dokokin sun haɗar da
1. Masu zuwa sallah Asham su ƙauracewa abubuwan da ba za su zama ba, amma babu laifi su fita da dardumar sallah domin tanadi.
2. Yakamata mutane da ke hallatar masallatan da ake gudanar da Tafseer suyi taka-tsan-tsan, tare da kai rahoton duk wani abu ko motsin da basu aminta da shi ba ga jami’an tsaro.
3. Dole ne masu ababen hawa su bi ka’idojin tuki, da gujewa tukin ganganci, domin tsira da rai da lafiya.
4. An haramtawa yara kanana marasa lasisi tuka ababen hawa wadanda suka hadar da mota, babur mai kafa Biyu, ko babur mai kafa uku kirar adaidaita sahu.
KU KUMA KARANTA:‘Yansanda sun fake da barazanar tsaro ne kawai don su hana Maulidin Tijjaniyya – Gwamnatin Kano
5. A kwai bukatar iyaye su runga raka ‘ya’yansu ko hadasu da manyan wanda suka mallaki hankali, a duk inda zasu shiga, a lokacin Azumi domin gudu bacewar yara ko kuma haduwa da wani hadari.
6. An kuma haramta hawa doki ba bisa ka’ida ba, dama gabatar da duk wasu tarukan da ba’a nemi izini ba.
7. An haramta amfani da wasa da wuta ko kuma buga wani abu mai kara a Lok Ramadan
Hukumar tayi kira ga al’ummar Kano su amfani da wannan wata mai girma, domin gabatar da addu’oin neman zaman lafiya a Jihar dama kasa baki daya.
A karshe hukumar Yan sandan sun kara jinjina da godiyarsu ga al’ummar Kano, bisa yadda suke basu goyon baya.