‘Yansanda a Abuja, sun gano wata matashiya da aka yi tsafi da ita a ɗakin Otal

0
9
'Yansanda a Abuja, sun gano wata matashiya da aka yi tsafi da ita a ɗakin Otal

‘Yansanda a Abuja, sun gano wata matashiya da aka yi tsafi da ita a ɗakin Otal

Rundunar ‘Yansandan babban birnin tarayya Abuja, ta samu nasarar gano wata Matashiya da wasu da ake zargin ‘yan fashi da Matsafa ne suka tsafeta a ɗakin Otal.

Kakakin rundunar a Abuja, SP Josephine Adeh, ce ta sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta aiko wa jaridar GTR Hausa a safiyar yau Lahadi, inda ta ce lamarin ya faru ne a ranar Jumu’ar da ta gabata, a wani dakil Otal dake yankin Wuse.

A cewar Adeh, “Jami’anmu sun isa dakil Otal din inda suke iske wata Matashiya me suna Promise Eze, ‘yan asalin jihar Ebonyi a daure a jikin Kujera baya ga like Bakinta da Bandeji harma ta fita daga hayyacin ta, hakan ne yasa suka dauke ta zuwa Asibitin gundumar Wuse inda likitoci suka ceto rayuwar ta”.

KU KUMA KARANTA:‘Yansanda a Abuja sun gano motar da aka sace ta hanyar amfani da na’urar bibiya

Kuma binciken mu a Otal din ya gano mana cewa kwana daya kafin faruwar lamarin, Matashiyar ta shiga dakin mutumin da ya ayyana kansa a matsayin Emmanuel Okoro daga jihar Legas.

Da take amsa tambayoyin ‘Yan Sanda, Matashiyar Promise ta ce sun hadu da mutumin ne a kafafen sada zumunta wanda ya ce mata sunan sa Alias Michael Prince, kuma yana aiki da wani kamfanin Mai dake jihar Delta, harma ya gayyace ta zuwa jihar Deltan amma taki zuwa wanda daga bisani suka amince su hadu a Abuja.

Kuma bayan ta je wajen mutumin yayi amfani da wasu abubuwa wajen yi mata wani siddabatu bayan ya raunata ta, Kafin daga bisani ya daure mata kafafuwanta da hannaye baya ga toshe mata Baki, inda ya cillata Bandaki ya kulle

Ta kuma kara da cewa kafin fitar sa taji yana waya da abokan mugun aikin nasa, inda yake shaida musu gashi nan zuwa wurin su kafin ya dawo ya karasa aikin nasa, harma ya tafi da Wayoyinta guda biyu.

Mafari kenan da Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja CP Olatunji Disu, ya ce tuni sun kaddamar da binciken da zai kai su ga gano wadannan bata-gari, ta yadda za’a gurfanar da su a gaban Kotu domin su fuskanci hukunci dai-dai da abinda suka aikata.

Haka kuma ya shawarci ‘Yan Mata da su dinga kula sosai wajen yin mu’amala da bakin fuskar da basu sani ba, harma ya bukaci dukkan mai wani rahoto na yadda zasu kama wadanda ake zargi ya tuntube su ta lambobin waya 08032003913 ko kuma 08107314192.

Leave a Reply