’Yansanda 5 sun rasu a wani hatsarin mota
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu ’yansanda guda biyar a wani hatsari da ya rutsa da su.
Hatsarin ya faru ne a kan hanyar Zariya zuwa Kano a ƙauyen Karfi.
Kakakin hukumar a Kano, ya ce, rundunar ‘yan sandan ƙaramar hukumar Kura ne, suka bayar da rahoton hatsarin.
Ya ce ya rutsa da motoci guda biyu: tirela da kuma wata mota ƙirar Toyota Hummer mai lamba 14B101KN, mallakin Kano Line.
KU KUMA KARANTA: Mutane 29 sun mutu a hatsarin jirgin kwale-kwale a Kongo
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:15 na safe kuma ya rutsa da mutum 15.
Sai dai ya ce mutum biyar sun mutu, yayin da wasu 10 suka samu raunuka.
Waɗanda hatsarin ya rutsa da su ‘yan sandan ne da ke kan hanyarsu ta dawowa daga aikin zaɓen da aka kammala a Jihar Edo.
Binciken farko na FRSC ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce ƙima.