Yankin Babanna na cikin tsaka mai wuya saboda rufe bodar Najeriya da Benin
Rashin buɗe Bodar Najeriya da ƙasar Janhuriyar Benin dake yankin Babanna a jihar Neja na ci gaba da jefa al’ummomin yankin cikin yanayi na damuwa sakamakon yadda harkokin kasuwanci su ka samu koma baya a tsakanin ƙasashen biyu
Tun a lokacin tsohuwar gwamnatin Shugaba Buhari ne dai aka rufe wannan boda sakamakon matakin da gwamnatin Buharin ta dauka na rufe iyakokin ƙasar ta ƙasa a wancan lokaci.
Iyakar ta Babanna dake ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja tana da Babbar Kasuwar ƙasa da ƙasa da ta haɗa ƙasashen Najeriya da Beni da kuma ƙasar Jamhuriyar Nijar harma da wasu ƙasashen Africa ta yamma,
A yanzu dai gwamnatin jihar ta kafa wata hukuma ta musamman da ta ke ƙira “Babanna Boda Deployment Agency” da nufin bunƙasa tattalin arzikin mazauna wannan yanki.
A wani taron masu ruwa da tsaki akan lamarin kasuwar ƙasa da ƙasa ta Babannan, mahalarta taron sun tattauna abubuwa guda uku da suka hada da buƙatar gwamnatin Najeriya ta sake buɗe wannan bode da kuma ƙara inganta hanyoyin zirga zirga da kuma tabbatar da ingantuwar tsaro.
A hirar shi da Muryar Amurka, Shugaban ƙaramar hukumar Borgu, Hon.Suleman Yarima kilishi ya bayyana cewa, dama suna da alaƙa mai ƙarfi a tsakanin yankin Faraku ta ƙasar Benin da kuma Borgu ta Najeriya saboda haka yace buɗe wannan boda zai taimaka wajan ƙara ƙarfin wannan dangantaka.
KU KUMA KARANTA: DR Congo da Zambia sun fara tattaunawa game da rufe kan iyaka
Suma dai Sarakuna iyayen kasa sun jaddada bukatar ganin hukumomi sun waiwayi yankin na Babanna ko baya ga buɗe-buɗe bodarma lamarin rashin tsaro na zama wata babbar barazana.
Tunda farko Wani jami,in hukumar Kwastan a Najeriya Ma’aruf Aliyu Goro da ya halarci wannan taro yace idan aka shawo kan matsalolin da yasa aka rufe Bodar a baya, za a buɗe ta nan bada jimawa ba.
Bayanai dai na nuna wannan yanki na Babanna yayi matukar komawa baya ta fuskar ci gaban tattalin arziki sakamakon rufe wannan iyaka na kusan shekaru shida zuwa bakwai.