‘Yan sandan Kano sun soma bincike kan zargin lakaɗa wa wani likita duka a asibitin Murtala

0
120

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta soma gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa wasu mutane na dukan wani likita a asibitin Ƙwararru na Murtala da ke cikin birni.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Litinin da tsakar dare.

‘Yan sandan sun ce bayanan da suka samu sun nuna cewa dangin wata mata mai juna biyu ne suka lakaɗa wa likitan mai suna Shehu Usman Abdulwahab duka bayan ta mutu a yayin da yake karɓar haihuwa.

Wannan lamari ya tayar da yamutsi a asibitin kuma bayan samun wannan rahoto ne aka tura tawagar ‘yan sanda wurin da lamarin ya faru nan-take, a cewar Kiyawa.

Ya ƙara da cewa daga bisani Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Mohammed Usaini Gumel ya ziyarci asibitin inda ya gana da jami’ai da masu ruwa da tsaki domin ganin halin da ake ciki.

KU KUMA KARANTA: An cafke lauya kan lakaɗa wa matarsa duka

“Ya tabbatar musu cewa rundunar ‘yan sandan Kano tana ɗaukar lamarin da matukar muhimmanci kuma tuni ta soma bincike a kansa. Kwamishinan ya umarci a kai ƙarin jami’ai domin tabbatar da tsaro a asibitin,” in ji kakakin rundunar ‘yan sandan.

Kiyawa ya ce “rundunar ‘yan sandan Kano ba za ta lamunci duk wani cin zarafi da barazana ga ma’aikatan kiwon lafiya ba waɗanda suke yin aiki babu dare babu rana domin ceto rayukan jama’a da kula da marasa lafiya”.

Leave a Reply