‘Yan sandan Iran za su dawo kama matan da suka karya dokar rufe gashin kansu

0
374

Daga Ibraheem El-Tafseer

‘Yan sandan Iran sun fara samame domin sanya ido kan matan da ke karya dokar rufe gashin kansu.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar ta ce ‘yan sandan na ci gaba da sintiri domin kamo mata da ke bijirewa dokar rufe gashin kansu a bainar jama’a.

A bara ne wasu da gwamnatin ƙasar ta kira da bara gurbi, suka jagoranci zanga-zangar ta da zaune tsaye a wani ɓangare na ƙasar ta Iran bayan mutuwar Mahsa Amini.

Bayan zanga-zangar, gwamnatin Iran ta yanke shawarar soke ‘yan sandan ɗa’a’. Aikin ’yan sandan ɗa’a shi ne tabbatar da ƙa’idojin shigar da tufafin Musulunci a ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Iran za ta dasa na’urorin ɗaukan hoto don kama matan da ba sa saka hijabi

Yanzu haka dai an samu labarin cewa ‘yan sanda za su sake fara sintiri a motoci da kuma ƙafa domin kamo waɗanda suka karya dokar. Bayan haka kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

Leave a Reply