‘Yan sanda sun kama wani ɓarawon mota

0
36
'Yan sanda sun kama wani ɓarawon mota

‘Yan sanda sun kama wani ɓarawon mota

Daga Ali Sanni Larabawa

Rundunar ‘yan sandar babban birnin tarayyar Najeriya, sunyi nasarar kama wani mutum da ake zargi da ƙwace wata mota ta hanyar amfani da bindiga, watanni uku da suka wuce.

Kwamishinan ‘yan sandar Abuja, Benneth Igweh ne, ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da wanda ake zargi a ranar Litinin.

Ya ce wanda ake zargin, mai suna Michael Uke, ya sace mota ƙirar Toyota Corolla mai lamba ABC 258 LD ta hanyar amfani da bindiga a ranar 2 ga watan Mayu, 2024, a kan hanyar Kuje.

KU KUMA KARANTA: Wasu matasa a Bauchi sun ƙone ɓarayin adaidaita sahu har lahira

‘Yan sandan sun bi sawun sa har zuwa wani otal dake yankin Jabi, inda suka same shi tare da motar daya sace.

‘Yan sandan sun kuma gano cewa wanda ake zargin ya sauya lambar motar zuwa AGD 146 JP.

A yayin binciken, sun gano na’urar POS, wuƙa, da kuma hular sojoji a wajensa.

‘Yan sandan na cigaba da gudanar da bincike  a kan lamarin.

Rundunar ta buƙaci mazauna yankin su riƙa sanar da su abubuwan da ke faruwa ta waɗnnan lambobin: 08032003913, 08028940883, 08061581938, da 07057337653.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here