‘Yan sanda sun kama matar da ta kwara wa mijinta tafasasshen man gyaɗa ta kwaɗa masa guduma ta gudu

0
329

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ribas ta sanar da cafke matar da ta yi wa mijinta wanka da tafasasshen man gyaɗa a jihar.

Matar mai suna Hope Nwala ana zargin ta da watsawa mijinta, Ekelediri Nwanko man gyaɗa kan wata ƙaramar jayayya, cewar Punch.

Nwala ta aikata laifin ne a ƙauyen Okehi da ke ƙaramar hukumar Etche a jihar bayan mijin ya kwanta bacci.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce matar na hannun jami’ansu, Newstral ta tattaro.

Grace ta ce jami’ansu sun yi nasarar kama matar ce bayan ta tsere ganin girman laifin da ta aikata.

KU KUMA KARANTA: Uwargida ta zuba wa maigida tafasasshen man gyaɗa yana cikin barci, ta kwaɗa masa guduma ta gudu

Ta ce “An kama matar kuma ta na hannun jami’anmu, an cafke ta ne a yau Alhamis 12 ga watan Oktoba.

“A yanzu haka ana kan bincike wanda da zarar an kammala za a ɗauki matakin da ya dace.”

Leave a Reply