Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce kimanin jami’an tsaro dubu 18,748 ne aka baza a fadin jihar domin gudanar da zaɓukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki na ranar 18 ga watan Maris.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labara na ƙasa a talata a Kano.
Ya ce ‘yan sandan da sauran jami’an tsaro za su samar da cikakken tsaro a runfunan zaɓe dubu 11,222 da ke mazaɓu 484 da ke fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan kwamitin tsaron zaɓe sun gana a Abuja
Dauda ya ce tuni aka bayar da umarnin gudanar da aikin tsaro ingantacce ga kwamandojin yankin da jami’an ƴan sanda na Caji-ofis domin aiwatarwa.
Ya kuma tabbatar da cewa ƴan sanda da sauran jami’an tsaro sun shirya tsaf don kare masu kaɗa ƙuri’a da jami’an INEC a lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe.
“Ina ba da tabbacin tsaro kashi 100 cikin 100 ga duk mazauna jihar masu bin doka da oda cewa za su yi zaɓe cikin yanci a ranar 18 ga Maris ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” in ji shi.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda dubu 18,748 aka jibge a Kano saboda zaɓen Gwamna […]
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda dubu 18,748 aka jibge a Kano saboda zaɓen Gwamna […]
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda dubu 18,748 aka jibge a Kano saboda zaɓen Gwamna […]