‘Yan sanda a Katsina sun kama matashin da ya sare hannun ƙanin mahaifinsa
Wani matashi da ya sari ƙanin mahaifinsa da adda a hannu, bisa zargin maita ya shiga hannun ’yan sandan a garin Jangefe da ke ƙaramar hukumar Ɓatagarawa a jihar Katsina.
Kamar yadda ya fada da bakinsa, matashin ya ce yana zargin ƙanin mahaifin nasa da maita, inda yake kama ’yan gidansu, ciki har da har da mahaifiyar matashin.
“Mahaifiyata ta kamu da rashin lafiya bayan shigowar shi ƙanin mahaifin nawa gidan, bayan ya fita, sai ta riƙa ambaton sunan shi ƙanin mahaifin nawa.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama wani ɓarawon mota
“Da ma duk wani ɗan gidanmu da ya kamu da rashin lafiya sai ya rika ambaton sunansa. Wannan ne ya sa nike zargin shi da yin maita,” in ji shi.
A cewarsa, ya je gidan kanin mahaifin nasa ne inda bayan ya yi mashi sallama ya fito ya nemi su kebe domin yana son magana da shi, amma sai ya ki yarda ya bi shi inda ya so su je.
Nan take ya bayyana mishi zargin da yake masa, sannan ya kai mishi sara da addar dake hannunsa, kuma ya same shi a hannu.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya shaida wa manema labarai a yayin gabatar da matashin cewa, bayan samun labarin abin da ya faru suka yi nasara kama ake zargi da saran ƙanin mahaifin nasa, kuma bayan sun gama bincike za su tura shi zuwa kotu domin yanke mishi hukunci.