‘Yan Majalisa Na Da Ikon Tabbatar Da Dokar Tsarin Zaben ‘Yar Tinke-Dokta Nasirudeen

0
306

Daga Isah Ahmed, Jos

Dokta Nasirudeen Usman, shi ne  Daraktan   Sashin horar da manyan ma’aikata na Sojoji da   manyan jami’an tsaro, na Cibiyar Nazarin Dabarun Mulki ta Kasa [NIPSS] da ke Kuru,  a Jihar Filato. Kuma masani  kan harkokin shari’a a Najeriya. A wannan tattaunawa da ya yi, da wakilinmu ya bayyana cewa ko Shugaban Kasa, bai sanya hanu kan dokar nan ta tsarin zaben ‘yan tinke, da ake ta dambarwa a kai ba. ‘Yan majalisar dattijai da ‘Yan majalisar wakilai ta tarayya, zasu iya tabbatar da wannan doka.

Ga yadda tattaunawar ta kasance

GTK: Mene ne zaka ce kan batun dokar nan, ta zaben ‘yan tinke  da ake ta dambarwa a kai?

Dokta Nasiruddeen:Maganar tsarin yadda jam’iyyu suke  fitar da ‘yan takararsu, doka ta basu hanyoyi guda biyu ne.

Jam’iyyu suna da zabi ko dai su fitar da ‘yan takararsu ta haryar    zaben ‘yan tinke, wadda wasu suke kira  kato bayan kato. Ta yadda dukkan ‘yan jam’iyya, wadanda suke da katin jam’iyyar zasu fito su zabi, wanda suke so ya yiwa wannan jam’iyya takara.

Ko kuma su bi hanyar zaben wakilan jam’iyya, wadda ake kira Deligete. Wato wasu ‘yan jam’iyyar da ake zabe,  a matakin Unguwa  da  matakin Karamar Hukuma da matakin Jiha, domin  su taru su zabi ‘yan takarar wannan jam’iyya.

To, matsalar da ake samu a nan  ita ce, zaka ga jam’iyyu sun  fi amfani da wannan tsari na Deligete. Kuma  zaka samu a cikin ‘yan takarar da suka tsayawa wannan jam’iyya, zaka sami wani ko shi ne yafi kowa lalacewa,  cikin ‘yan takarar, idan yana da kudi zai iya sayen dukkan wadannan Deligete. Zaka ga mafiyawan mutanen jam’iyyar ba shi suke so ba,  amma ya bayar da  kudi ya ci wannan zabe.

Ko kuma ace gwamnati a jiha ko a Karamar Hukuma, su ce dole ga wanda suke so, ya tsaya takara saboda haka dole a tursasawa  Deligete su zabi wannan dan takara.

Kuma babbar matsalar  su kan su Deligete din, ba zabarsu ake yi ba. Ana zama ne wadanda suke ganin sune masu ruwa da tsaki, ko gwamna ko Shugaban Karamar Hukuma su ce wane da wane sune shugabannin jam’iyya. Kaga baki daya, an dauke ruhin damakoradiya a nan.

 Don haka idan da aka zo babban zabe, sai dai mutane su zabi wanda yafi dama dama, cikin rubabbun da jam’iyyu suka tsayar masu takara.

Wannan abin shi ne ya jawo cece kuce ake ganin cewa, idan ana son ayi damakoradiyar ne a fara tun daga zaben ‘yan takarar jam’iyyu.

Wato ya zamanto wajen tsayar da ‘yan takara na jam’iyyu, ba mutum daya ko biyu ko uku ne zasu fitar da ‘yan takara ba. Jama’a magoya bayan jam’iyya ne za a basu dama, su zabi ‘yan takara.

Don haka ake ta dambarwa, tsakanin ‘yan majalisa da Shugaban Kasa. Inda ‘yan majalisar tarayya na Sanatoci da na tarayya, suke cewa ayi zaben kato bayan kato.

GTK: Ganin Shugaban Kasa bai sa hanu kan wannan doka ta zaben ‘yan tinke ba, kana ganin ‘yan majalisa suna da damar su tabbatar da wannan doka?

Dokta Nasiruddeen: A tsarin mulkin Najeriya  zasu iya. Domin yadda yin doka yake a kasar nan, abu ne guda biyu dole sai sun faru. Wato sai majalisun nan guda biyu, na Dattijai da na Wakilai na tarayya sun yarda cewa abu kaza da abu kaza ne, zai zama doka. Idan sun amince a tsakaninsu sai su turawa Shugaban Kasa. Shi kuma ya amince ya sanya hanu, kafin abin ya zama doka. Idan aka kai masa yana da damar ya ce abu kaza da abu kaza da aka kawo,  bai yarda da shi ba, saboda dalilai kaza da kaza, ya mayar masu. Idan bai yi haka ba, har  kwanaki 30, zasu yi amfani da damar da tsarin mulki, ya basu su kawar da wannan dama, ta Shugaban Kasa su zartar da wannan doka.

To yanzu halin da ake ciki game da wannan doka, Shugaban Kasa ya yi korafe korafe ya mayarwa masu,  ya ce su sake nazari.

A cikin korafe korafen Shugaban Kasa akwai yanayin yadda Kasar nan ta tsinci kanta a ciki, na rashin tsaro da makudan kudaden da za a kashe, wajen gudanar da wannan zabe.

Babu shakka akwai wadannan abubuwa da Shugaban kasa ya fada, amma ni  kullum abin da nake fada, shi ne idan matsala ta taso sai a sanya ta a ma’auni, aga wanne ne yafi illa? Shin Illar da za a yiwa damakoradiya ta hanyar dauki dora ne ko kuma illar wahalar da za a sha idan aka yi zaben kato bayan kato tafi?.

 Sai a gwada aga wanne ne yafi, Idan aka ga wanda yafi sai a dauka.  

Amma dai abu mai mahimmanci, zaben nan na shekara ta 2023 ya karato, don haka dole ne mu yi kokari mu san abin da zamu yi, na tsarin doka. Domin hukumar zabe ta kasa INEC, ta sami isasshen lokaci zata tsara abubuwan ta.

Yanzu dai  Shugaban Kasa ya mayar masu, zasu iya cewa sun yi nazari kan korafe korafen da ya yi  sun yi kwaskwarima  ya sanya hanu, idan kuma suka ce su suna nan, kan matsayarsu zasu iya sake mayar masa, idan bai sanya hanu ba, cikin kwana 30, zasu iya tabbatar da wannan doka.

GTK: Ya ya kake ganin yanayin tafiyar harkokin Shari’a a wannan gwamnati?

 Dokta Nasiruddeen: Wato ni a fahimtata, idan aka sami matsala a cikin al’umma, ko gyara  yana shafar kowanne Bangare. Kasar nan yanzu muna cikin wani hali na rudani, musamman a siyasance. Idan aka sami irin wannan, dole wannan al’amari ya shafi kowanne bangare.

Babbar matsalar ita ce bangaren shari’a, wanda  shi ne ake gani  a matsayin yaki na karshe.  Domin komai lalacewar al’umma,  ana sa ran  idan aka yiwa mutum, wani abu wanda ba dai dai ba, idan yaje sashin shari’a, za a kwatar masa hakkinsa.

To, a  nan zan iya cewa ana kokartawa, gwargwadon hali a wannan gwamnati. Amma  ina tabbatar maka, gurbacewar  al’ummarmu bai bar bangaren shari’a ba.

GTK: Ana  kukan cewa akwai wasu manya a Kasar nan  da suke  gaban kotuna kan tuhumar aikata laifuffuk,a amma an ji shuru kan irin wadannan shari’o’ mene ne kake ganin ya kawo haka?

 Dokta Nasiruddeen: Wato abubuwa da yawa ne suke kawo wannan abu. Yanzu  kasar nan  da zarar an yi zargin wani ya yi laifi, musamman saboda yadda cin hanci da rashawa ya addabi al’umma. Don haka mutane da dama, suna bukatar suga an yankewa wannan mutum, da ake zargi hukumci an kai shi gidan yari, ko kuma wani abu makamancin haka.

 To amma ita shari’a a wajen ta, zargi daban hukumci tabbatar da zargi daban. Sai an yi zargi an bi matakan da ake tabbatar da zargin, idan an tabbatar da zargin nan, sannan hukumci ya biyo baya.

To inda ake samun matsalar, matakan da ake bi, na tabbatar da zargin  sune ke da matsala. Kuma wannan yana da nasaba ne da irin tsarin shari’ar da muke bi. Duk da akwai gyare gyare da aka yi, daga baya bayan nan, domin a cire wasu abubuwa na yadda ake yi a tabbtar da mai laifi. Misali akwai sabon kundi wanda tun a shekara ta 2015, aka fito da shi wanda ya kun shi doka da aka yi a gwamnatin tarayya,  kuma  jihohi da dama sun fara aiki da wannan kundin doka.  Manufar wannan kundin doka, shi ne a sassauta matakan da ake bi, na tabbatar laifi ga wanda ake zargi.

Hukumar ‘yan sanda ko hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kamar EFCC ko ICPC. Sune idan an kawo korafi a wajensu, ko kuma  kan tafiyar da aikinsu,  idan suka gano an yi wata barna, zasu dauki matakai da bincike don ganin an tabbatar da wannan laifi, da ake korafi da shedu  su gabatarwa kotu.

 Idan ba abi wannan ba, ita kotu  ba zata ce, da zarar an kawo wanda ake tuhuma da aikata laifi, nan take aje a garkame shi ba.  Matsalar da ake samu ke nan.

Kuma musamman sha’ani na tuhuma kan cin hanci da rashawa.  Zamani ya kawo sarkakiya  na tabbatar da wadannan laifuffuka. Kuma wadanda ake zargin nan, suna da kudaden da zasu amfani da su, don kawo cikas kan matakan da ake bi wajen tabbatar da zargin da ake yi masu. Wannan wani abu ne wanda ba karamin aiki ne ba.

GTK: Wadanne hanyoyi ne kake ganin za abi a warware wadannan matsaloli?

 Dokta Nasiruddeen: Ni a ra’anyi duk wanda aka ce ya saci kudin gwamnati har Naira miliyan 100, ko sama da haka. Idan kaje kace kana bincikensa, ina tabbatar maka zai iya salwantar da rabin wannan kudi, domin yaga cewa ba a hukumta shi ba. Kuma ba kowanne mutum ne zai kawar da kai, daga karbar  kan cin hanci da rashawa ba a wannan lokaci da muke ciki.

Don haka ni a ra’ayina, abi matakan  kada  a bar barnar ta faru. Domin idan a yau aka dada tsaurara hanyoyin da ake bi, wajen kashe kudaden gwamnati. A tabbatar cewa duk Naira daya da aka kashe ta gwamnati   an san inda aka kashe ta. Kaga ba za a zo kan cewa ana zargin wani ba, kuma ana son a bincike shi.

Muna da wata Hukuma da gwamnatin tarayya ta kafa, wadda ake kira Fiscal Responsibility. Wannan hukuma ce da aka kafa ta domin tabi, diddigin yadda ake tsarin kasafin kudi da yadda ake sakin wannan kudi da yadda ake aiwatar da ayyuka.

Ya kamata wannan hukuma ta rika bibiya, tun daga matakin tsara kasafin kudi, da yadda ake gudanar da aikin  da aka bayar da yadda aka kashe kudin.

Ina tabbatar maka, idan da an baiwa  wannan Hukuma  karfin da ya kamata a doka,   tayi aikin ta kamar yadda doka ta ce. Wallahi Hukumomin EFCC da ICPC zasu  rasa aikin da zasu yi. Kuma da yawa a matakan jihohi, gwamnoni sun kafa irin wadannan hukumomi. Amma ba a bari su yi aikin da ya kamata.

 Don haka ni a ra’ayina ayi abin da za a hana barna, kafin ace a bari sai mutum ya aikata barnar, sannan ace za a kama mutum ayi bincike.

GTK: Karshe wanne sako ne kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya?

 Dokta Nasiruddeen: Yadda muka tsinci kanmu a kasar nan, abu ne mai ban tsaro da takaici. Duk ni’imar da Allah yake yiwa al’umma a duniya, Allah ya yiwa kasar nan. Amma kullum muna cikin waiyo waiyo.

 Ni a ganina wannan hali da muka shiga, ba abu ne da za a dora shi ga shugabanni kadai ba. Ya kamata mu a matsayinmu na ‘yan kasa, mu dubi kanmu mu dubi mu’amalarmu da iyalanmu da sauran abokanan zamanmu. Kuma mu sani babu wanda zai zo, ya gyara mana kasarmu dole mu ne zamu tashi mu hada hanu mu gyara kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here