‘Yan kasuwa a Kano sun koka kan tsadar Burodi duk da sauƙar farashin fulawa

0
19
'Yan kasuwa a Kano sun koka kan tsadar Burodi duk da sauƙar farashin fulawa

‘Yan kasuwa a Kano sun koka kan tsadar Burodi duk da sauƙar farashin fulawa

Daga Jamilu Lawan Yakasai

A yayin da watan Ramadan ke ƙara gabatowa, manyan ’yan kasuwa a Kasuwar Singa dake Jihar Kano sun koka kan yadda ƙananan ’yan kasuwa ke ci gaba da sayar da kayayyaki a farashi mai tsada duk da saukar farashin kayan a wurin manyan dilolin.

Manyan ’yan kasuwar sun yi zargin cewa har yanzu wasu ’yan kasuwa da masu gidajen burodi da masu sayin Gurasa na ci gaba da sayar da kaya akan tsohon farashi bayan kaso ɗaya bisa uku na farashin kaya ya sauka a kasuwar.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta hana CBN da RMAFC riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin Kano

Hakan yasanya mazauna Kano da dama ke cigaba da shan wahalar rayuwa, sakamakon sukan sayan kayan masarufine a wajen kananan ‘yan Kasuwa mai makon shiga Kasuwa wajen manyan diloli.

Sai dai Malamai da dama na cigaba da jan hankalin ‘yan kasuwan wajen saukakawa al’umma, domin samun riba mai albarka, dama samun tsira a ranar gobe alkiyama.

Leave a Reply