’Yan Kannywood da dama sun ƙaurace wa taron da Hisbah ta gayyata a Kano

0
584

’Yan Kannywood da dama musamman ma fitattun jarumai da daraktoci da furudososhi sun sa kafa sun shure gayyatar da Hukumar Hisbah ta yi musu domin tattaunawa da su a jiya Litinin.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, ’yan masana’antar fina-finan ƙalilan da ba su wuce 30 ba ne suka halarci amsa goron gayyatar.

Tun dai a ranar Jumaar da ta gabata ne Hukumar ta Hisbah ta bakin Mataimakin Babban Kwamandanta kan Ayyuka, Dokta Mujahideen Aminudden ta bayar da sanarwar cewa za ta tattauna da ’yan fim ɗin ne don yin gyara ga ayyukansu a ci gaba da ayyukan da Hisbar ke yi na ‘Operation Kawar da Badala.’

Sai dai Shugaban ƙungiyar jarumai ta Kannywood Alasan Kwalle ya bayyana rashin jin daɗinsu game da gayyatar ta Hisbah wanda ya ce kamata ya yi ta aika musu takardar gayyata a hukumance.

“Bai kamata Hisbah ta kira mu ta kafar rediyo ba wanda ya yi kama da neman masu laifi. Ko a baya mun zauna da Hisbah wanda kuma mun fa’idantu da tattaunawar.

KU KUMA KARANTA: Yau Hisbah za ta yi zama da ’yan Kannywood

“A yanzu ma za mu halarci zaman matukar dai Hisbar ta gyara kuskurenta.”

Sai dai Babban Kwamandar Hisbar, Sheikh Aminu Daurawa ya ce sun aike wa ’yan fim din takardar gayyata ta hannun Shugaban Hukumar tace Fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, Abba Almustapha.

“Mun sanar ta rediyo ne kawai don amfanin alumma amma ba wai gayyatarsu muka yi a rediyo ba,” in ji Daurawa.

Da yake jawabi a wajen taron, Shaikh Daurawa ya bayyana cewa Hisbar ta damu game da yadda baƙin ƙananan ’yan mata ke kwararowa jihar da sunan shiga fim inda suka yi sansani a wurare daban-daban suna aikata baɗala.

“Ba mu so mu kai musu sumame don haka muke so ku shiga cikin lamarin don yi wa tufkar hanci.”

Daurawa ya ƙara da cewa Hukumar tana son ’yan fim ɗin su gyara wasu kura-kurai da suke yi a fina-finai musamman yanayin sanya tufafi da mummunan lafazi wanda zai iya ɓata tarbiyyar al’umma.

“Mun lura ba wai kawai jarumai ne ke taka rawa a fina-finai ba domin a lokuta da dama jaruman kan yi ƙorafi cewa duk abin da suke a fim darakta da forudusa ne suke sanya su don haka muka haɗa da su a cikin gayyatarmu don mu sami fahimtar juna.”

A jawabinsa, jarumi Abdullahi Amdaz (Excellency) ya bayyana cewa suna sane da irin abubuwan da ke faruwa na assha a masana’antar, wanda kuma ya ce a shirye suke su gyara kurakuransu.

A yayin zaman, an ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwa tsakanin ɓangarorin biyu don laluɓo hanyoyin da za a kawo gyara a harkokin masana’antar.

Leave a Reply