‘Yan hamayya a Chadi sun nemi Mahamat Idriss Deby ya janye daga tsayawa takara a zaɓen 2024

0
112

Gamayyar ƙungiyoyin hamayya da masu zaman kansu da ba sa ɗauke da makamai a Chadi ranar Laraba ta yi ƙira ga shugaban ƙasar Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya gaji mulki bayan mutuwar mahaifinsa a 2021, ya janye daga tsayawa takara a zaɓen wannan shekarar.

Gammayar mai suna Wakit Tamma ta zargi ƙasashen duniya, musamman Faransa, da goyon bayan mulkin gado a Chadi da kuma mara wa Janar Mahamat Deby baya a “shirinsa na kwace mulki, ciki har da amfani da ƙarfin soja”.

An naɗa Mahamat mai shekara 37 a matsayin shugaban ƙasa shekaru biyu da suka wuce bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno a wani gumurzu da suka yi da ‘yan tawaye a fagen yaƙi. Ya kwashe fiye da shekara talatin yana mulki.

Ƙasashen duniya sun yi ƙira ga ɗansa ya gudanar da zaɓe cikin watanni 18 kamar yadda ya yi alƙawari.

Sai dai ya ƙara shekaru biyu a kan alƙawarin da ya yi na miƙa mulki ga farar-hula.

KU KUMA KARANTA: Sudan ta kori ma’aikatan jakadancin Chadi daga Khartoum

Babbar jam’iyyar adawa ta ƙasar wadda kuma ita ce ƙungiya mafi girma da ke riƙe da makamai ta ƙaurace wa wani shirin tattauawa na ƙasa da aka gudanar.

Wakit Tamma ta fitar da sanarwa ranar Laraba da ke ƙira ga Janar Deby da kada ya tsaya takara a zaɓen da ke tafe domin ya zama mai kishin ƙasa.

Ta zargi Faransa da “yin katsalandan a harkokin ƙasar nan… a yunƙurin na ƙara ƙarfi a yankin Sahel”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here