Wasu ’yan bangar siyasa sun buɗe wa jama’a wuta tare da sace kayan zaɓe a yayin da ake gudanar da zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.
’Yan bangar siyasanan sun kai harin ne a wasu rumfunan zaɓe a ƙananan hukumomin Ija ta Kudu da kuma Sabgama, insa suka rika harbe-harbe suna tafiya da kayan zaɓe.
Maharan sun fatattaki masu zaɓe suka kwashe kayan zaɓen a yankin Agorogbene, rumufanan zaɓe masu lamba 6, 7 da 8 gunduma ta 11 da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu.
Masu zaɓe sun nemin yin fito-na-fito da ’yan bangar siyasan, amma suka mayar da martani da harbe-harbe.
Da misalin karfe 9 na safe wasu ɓata-garin sun kai hari a cibiyar tattara sakamakon zaɓe inda suka yi awon gaba da kayan zaɓen biyar daga cikin mazaɓu bakwai.