‘Yan bindiga sun yi garkuwa da likita a Kogi

0
229

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani likita, Austin Uwumagbe, Daraktan Asibitin Nasara-Annex da ke Ogaminana, a ƙaramar hukumar Adavi a jihar Kogi.

Jaridar ta samu labarin cewa an ga Dakta Uwumagbe a ranar Talata bayan ya gama aiki ya nufi gida.

Wata majiya daga asibitin ta ce waɗanda suka yi garkuwa da shi sun tuntuɓi iyalansa, inda suka buƙaci a ba shi maƙudan kuɗaɗen kafin ya samu ‘yancinsa.

Ƙungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Kogi ta tabbatar da sace Dakta Uwumagbe a wata sanarwa da ta fitar jiya a Lokoja.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun ƙuɓutar da ɗaliban jami’a shida waɗanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Zamfara

Wata sanarwar haɗin gwiwa mai ɗauke da sa hannun shugaban NMA na jihar, Dakta Baoku Olusola, da Sakatare, Dakta Emmanuel Bola Jonah, sun ce an yi garkuwa da abokin aikin nasu jim kaɗan da barin asibitinsa a ranar Talata.

“An ce an sace shi ne da motar sa, wata toka mai lamba 406 Peugeot mai lamba DAV 561 AA, da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Talata,” in ji NMA a cikin sanarwar.

Yayin da NMA ta yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da neman a gaggauta sakin ɗan uwansu da aka yi garkuwa da shi, hukumar ta yi ƙira ga jami’an tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don ganin ɗan nasu ya ƙwato masa ’yanci.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Aya, bai mayar da martani ga saƙon tes ba da kuma ƙiran hakan.

Leave a Reply