‘Yan bindiga sun sace fasinjojin Abuja a jihar Kogi

0
234

Wasu da ba a bayyana adadinsu ba a cikin wata motar bas mai kujeru 18 an yi zargin an sace su a Ochadamu kan hanyar Anyigba-Itobe a karamar hukumar Ofu a jihar Kogi.

Wani wanda aka yi abin akan idon shi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yamma, a ranar Litinin a wani wurin da ake garkuwa da mutane a kan babbar hanya.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan da yawansu sun yi ta harbin motar bas ɗin da aka ce ta nufi Abuja daga yankin Gabashin ƙasar inda suka tura fasinjojin cikin daji.

Mazauna yankin sun ƙara da cewa, ayyukan garkuwa da mutane a tashar Ochadamu ya ragu matuka, amma sun dawo a baya-bayan nan, bayan an cire shingen binciken sojoji da ke yankin,sakamakon wani mummunan hatsari da ya faru a babbar hanyar.

Jami’an tsaro da ’yan banga a yankunan, sun yi ta ƙoƙarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su,tun bayan faruwar lamarin.

KU KUMA KARANTA:Yan sanda sun kama dattijo da ke yiwa ‘yan ta’adda maganin bindiga

Mai baiwa gwamna Yahaya Bello shawara kan harkokin tsaro, kwamandan sojojin ruwa Jerry Omodara (murabus), ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, yana mai cewa gwamnatin jihar na kokarin kare abkuwwar hakan.

Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta sanya isassun matakan da za a bi domin daƙile yawaitar ayyukan ta’addanci a yankin.

Ya ce tun da ’yan ta’addan sun ƙara dawowa a kan titin, gwamnati za ta sauya matakan da ta ɗauka, inda ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za a kawar da ɓarayin.

“Mun yaƙe su; za mu yaƙe su, kuma za mu ci gaba da yaƙar su, har sai an ci galaba akan su” inji shi.

Ya ce an sanar da jami’an tsaro kuma za su yi abin da ya kamata.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a bayyana ko bas din a cike ta ke ko a’a ba.

Leave a Reply