‘Yan bindiga sun nemi kuɗin fansa kan ɗaliban da suka sace a kai har Kogi

1
436

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ɗalibai hudu na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi, da ke Lokoja, da kuma direban motar su, a kan titin Akunnu-Ajowa a ƙaramar hukumar Akoko ta Arewa-maso-gabas ta jihar Ondo a ranar Juma’a.

An ce ɗaliban suna tafiya gida ne domin zuwa hutun kiristimeti, sai ‘yan bindigar suka kama su a kan hanya suka ja su cikin daji.

Rahotanni sun nuna cewa sa’o’i kaɗan bayan sace ɗaliban, ‘yan fashin sun tuntuɓi iyalan waɗanda abin ya shafa, inda suka buƙaci a ba su kuɗi naira miliyan 16 kafin su sako su.

Wata majiya a unguwar Ajowa Akoko ta ce, “masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalansu kuma suna neman Naira miliyan 3 akan ko wane mutum guda da suka yi garkuwar daga cikin ɗaliban inda suka sanya naira miliyan 4 akan direban su.”

KU KUMA KARANTA:Yadda mata da miji sukayi garkuwa, tare da kashe mai hotel bayan sun karɓi kuɗin fansa miliyan 15

Wani shugaban al’umma kuma tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Akoko ta arewa maso yamma, Mista Ajayi Bakare, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce iyayen ɗaliban sun gargadi direban motar da kada ya bi hanyar da aka yi garkuwa da su, domin hanyar ta yi ƙaurin suna wajen yin garkuwa da mutane da fashi da makami.

Kwamandan rundunar ‘yan sandan yankin Ikare na jihar Ondo, Muri Agboola, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’ansa sun yi ta shiga dazuzzukan da ke kan titin Akunnu-Ajowa Akoko domin ceto ɗaliban da aka sace.

1 COMMENT

Leave a Reply