Gwamnatin Filato ta ce wasu ’yan bindiga da ke addabar al’umomin karamar hukumar Wase da ke jihar sun mika mata bindigoginsu ƙirar AK47, bayan wata tattaunawar sulhu.
Mai bai wa Gwamna Caleb Mutfwang shawara na musamman a kan harkokin tsaro kuma kwamandan Operation Rainbow, Birgediya Gakji Shippi, ya ce mika makaman ya biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da ’yan bindigar.
Ya ce baya ga bindigogi kirarAK47, ’yan bindigar sun mika wasu nau’ukan makaman, wanda hakan ke nuna aniyarsu ta samar da zaman lafiya ta hanyar kwance ɗamara.
KU KUMA KARANTA: Yadda aka kama dilan makaman ’yan ta’adda a tashar mota a Taraba
Ya ƙara da cewa, ’yan bindigar ba su mika bindigogin kai tsaye ba saboda fargaba, amma sun yi hakan ne ta hanyar masu shiga tsakani yayin tattaunawar.
“Baya ga manyan bindigogi da ’yan bindigar suka bayar, sun miƙa wasu nau’ikan makaman,” inji Shippi.
Ya ƙara da cewa, ana ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa gwiwar ’yan bindigar su miƙa makamansu bisa raɗin kansu.
Sa’annan ana rarakar waɗanda ba su miƙa wuya ba ana kuma ƙwato makaman wasu ƙungiyoyin ’yan ta’addar domin rage kai hare-hare a Ƙaramar Hukumar Wase.