‘Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir, Isa Bawa
‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir na garin Gatawa, Alhaji Isa Bawa, sun kashe shi.
A cikin wannan makon ne sarkin aka ga sarkin a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya ‘yan bindigar kuɗin fansar da suka buƙata, inda ya ce idan wa’adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.
Mako uku da suka wuce ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da sarkin a yankin Kwanar Maharba lokacin da yake kan hanyar komawa gida bayan halartar wani taro a cikin garin Sokoto.
A hirarsa da BBC, Shuaibu Gwanda Gobir, wanda shi ne magajin garin na Gobir kuma ɗaya daga cikin masu naɗin sarki, ya ce labari ya ishe su cewa masu garkuwar sun kashe sarkin ne a ranar Talata.
KU KUMA KARANTA: Al’ummar Gobir sun shiga zullumi bayan fitowar bidiyon basarakensu da aka sace
“Labarin da na samu shi ne ‘yan bindigar sun harbe shi ne tun a jiya [Talata] bayan la’asar, kuma waɗanda suka je tattauna biyan kuɗin fansa ne suka ga gawar sarkin a kwance,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa zuwa lokacin da aka yi magana da shi ba su karɓi gawar mai martaban ba tukunna.
Kazalika, ya ce akwai ɗan sarkin mai suna Kabiru da aka yi garkuwa da su tare, kuma abin da suka saka a gaba kenan yanzu.
Magajin garin ya ce: “A ranar Talata da safe an kira shugaban masu garkuwar har ma yana tambaya game da kuɗin fansa. Da aka nemi a yi magana da sarkin sai ya ce yana can yana jin ɗumi a gefen wuta.
“Da aka yi magana da Kabiru ya tabbatar da cewa sarki na can yana jin ɗumi, amma ya yi ta roƙon a biya kuɗin fansa domin kuɓutar da su.”
Wani ɗan sarkin na Gobir ya ce an yi wa mahaifin nasa kwanton-ɓauna ne a yankin Kwanar Maharba yayin da yake komawa gida.
“‘Yan bindigar sun fara harbi kan mai uwa da wabi lokacin da suka hangi motar mahaifin namu, abin da kuma ya janyo fashewar tayoyin motar da karkatar da hankalin direbansa har ta kai ya tsaya,” in ji ɗan sarkin.
Majiyoyi daga Sabon Birni sun ce an yi garkuwa da ƙarin mutum biyar a yankin a ranar da aka sace sarkin.