‘Yan bindiga sun kashe mutane 5 a iyakar Nijar da Najeriya

0
28
'Yan bindiga sun kashe mutane 5 a iyakar Nijar da Najeriya

‘Yan bindiga sun kashe mutane 5 a iyakar Nijar da Najeriya

‘Yan bindiga sun kai hari a kan iyakar Nijar da Najeriya, inda suka kashe mutane biyar tare da jikkata wani daya a garin Dambu da ke ƙaramar hukumar Bazaga ta gundumar Birni N’Konni, sannan suka sace dabbobi da dama a garin.

Wannan lamari dai ya faru ne a daidai lokacin da damuna ke ci gaba da kankamawa a yankuna da daban-daban na Jamhuriyar Nijar.

An dai juma ba a ji ɗuriyar ‘yan bindiga a kan iyakokin Nijar da Najeriya ba, inda suka afkawa al’ummar garin Dambu da ke cikin ƙaramar hukumar Bazaga.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun sace ‘yan jarida 2 da iyalansu a Kaduna

Hakimin garin Dambu Halidu Assoumane ya ce maharan sun shigo garin da kusan karfe goma sha biyu na daren ranar Asabar, inda suka shigo a kafa, kafin su buɗe wuta da manyan bindigogi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wani da yake cikin mawuyacin hali yanzu haka a asibitin Galmi.

Ya ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da dukiya mai yawa da suka hada da rakuma da shanu kafin jami’an tsaro su isa wurin.

A kwanakin baya dai shugaban gundumar Birni N’Konni, kuma shugaban majalisar tsaron wannan yanki, Kaptin Abubakar Ali Shina, ya yi kira ga mutanen garuruwa da ke kan wadannan iyakokin da su dauki matakan kula da abin da ke kai komo da ma kariya, kamar irin yadda babban birnin yakin na N’Konni ya kafa kwamitocin ‘yan kato da gora, domin samun damar kare kai tare da gaugauta sanar da jami’an tsaro.

Shi ma masanin harakokin tsaro, Malam Yusha’u Abdullahi, ya ce yana da kyau mutanen garuruwan da ke wannan yankin su kafa kwamitocin tsaro don kare garuruwan su, kamar yadda makwabtansu na Najeriya ke yi, wanda da zarar sun ga motsi abun da ba su yarda da shi ba su gaggauta sanarwa da jami’an tsaro don su kawo musu ɗauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here