Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari ofishinta da ke ƙaramar hukumar Enugu ta kudu, yayin da ya rage kwanaki 39 kacal a gudanar da zaɓukan wannan shekarar (2023).
Kwamishinan hukumar INEC na kasa, kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa kuri’a, Festus Okoye, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a Abuja ranar Litinin, ya ce an kai wa ofishin hari ne a ranar Lahadi.
A baya dai INEC ta bayar da rahoton kone-kone biyar a ofisoshinta da ke Enugu tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022.
Waɗannan sun haɗa da ƙone-ƙone da ɓarna da ‘yan bindiga suka yi a ofishinta na ƙaramar hukumar Udenu a ranar 13 ga Mayu, 2021, ofishin hedikwatar jihar a ranar 21 ga Mayu, 2021 da ofishin ƙaramar hukumar Ugbeeeze ta Kudu a ranar 23 ga Mayu, 2021.
KU KUMA KARANTA:Yan ta’adda sun ƙona Ofishin INEC a Ogun
Mista Okoye ya ce, Kwamishinan zaɓe na INEC, REC, na Jihar Enugu, Dr Chukwuemeka Chukwu, ya ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai wa ofishin hari da misalin karfe 9.12 na dare, ran Lahadi.
“An lalata kofar jami’an tsaro, an yi sa’a maharan sun kasa samun damar shiga babban ginin, sakamakon ɗaukin gaggawar da jami’an ‘yan sanda da na Sojoji na runduna ta 82 suka kai.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar da kuma REC da kan su suna wurin, nan take suka samu labarin harin.
“A cikin ‘yan sandan biyu da aka tura domin kare ginin, ɗaya daga cikinsu ya rasa ransa, yayin da ɗaya ya samu raunuka kuma yana samun kulawa,” in ji shi.
Mista Okoye ya yi addu’ar Allah ya jikan ɗan sandan da ya rasu, ya kuma baiwa waɗanda suka jikkata sauƙi cikin gaggawa. Ya ce yayin da za a sake gina kofar da aka lalata, INEC na ci gaba da shirye-shiryen zaben 2023 a jihar Enugu da ma ƙasar baki daya kamar yadda ta tsara.
Mista Okoye ya ce jami’an tsaro na binciken lamarin,ya kuma ƙara da cewa, an kira taron kwamitin tuntuɓa tsakanin hukumomi kan harkokin tsaro, ICCES, a jihar Enugu wanda REC da kwamishinan ‘yan sanda suka jagoranta domin tattaunawa kan sabon lamarin.
Ya ce taron kuma an yi shi ne don tsara wasu dabarun inganta ofisoshin da kuma kare ma’aikata da kayan aiki.