‘Yan bindiga na bautar da mutane a jihar Katsina

0
149

Jama’a a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina sun ce sun shiga tsaka mai wuya sakamakon yadda ‘yan bindiga suka mamaye garuruwansu, kuma suka mayar da su tamkar bayi.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun ƙwace gonakin jama’a, tare da tilasta wa mutanen garuruwan yi masu shuka da huɗa da ma sauran ayyukan gona.

Yanzu haka dai jama’ar da ‘yan bindigar suka mamaye a yankin ƙaramar hukumar Faskarin ta Najeriya suna cikin ƙunci da damuwa.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidawa BBC cewa ‘yan bindigar suna shiga ƙauyuka kuma su yi abin da suke so, kuma a lokacin da suke so.

Ya ce ‘‘A yanzu maganar da ake a cikin firamare ɗin Kogo ‘yan bindiga ne a ciki zaune, in an yi abinci a kai masu, in suka ga yarinya su ɗauka, in kuma ka yi magana su kashe ka.’’

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro sun halaka ƴan bindiga da ƙwace makamansu da babura a Kaduna

Mutumin ya ce mazauna yankin suna biyayya ne ga ‘yan bindigar saboda ba su da wani zaɓi na daban.

‘‘tashin farko dai suka sa aka haɗa masu kuɗi cikin yarjejeniyar da aka yi, da kuma gonakin da suka ware waɗannan ba za a noma ba, su za a nomawa. Duk lokacin noma za mu je can, mu yi masu huɗa mu yi masu noma, mu yi masu huɗa, su faɗa mana abin da za a noma, mu yi noma kuma idan lokacin girbi ya yi mu kwashe mu basu. Sun mai da mu tamkar bayi a cikin wannan yanki, idan ka yi kaifi a hukunta ka’’

Ya ce ƙauyukan yankin da suka haɗa da Birnin Kogo da ‘Yar-tsamiya da Kahi da Fankama da Hayin Dungu da kuma Gobirawa duk ƙarƙashin ikon ‘yan bindigar suke, waɗanda ke ci gaba da murgunawa jama’a.

Dakta Nasir Mu’azu, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina ya ce gwamnatin jihar ta farga da wannan lamari.

‘‘Mutane a irin waɗannan ƙauyuka sun je sansanin ‘yan gudun hijira, to kuma wasu da yawa ba za su iya haƙuri da zaman sansanin ba don haka sai suka koma ƙauyukan su, suna ci gaba da zama bisa ga yadda ‘yan bindigar suke ta gallaza masu’’

Dakta Nasir ya ce gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa yana aiki tuƙuru don kula da mutanen da matsalar tsaron ta tilasta masu yin hijira da kuma tabbatar da tsaro a faɗin jihar.

Gwamnatin jihar Katsina dai ta lashi takobin magance matsalar tsaro da ta dabaibaye garuruwa da ƙauyuka da dama na jihar. Kuma ko a kwanan nan sai da ta ƙaddamar da rundunar sintiri ta farar hula don taimakawa wajen tabbatar da tsaro.

Leave a Reply