Daga Nusaiba Hussaini
Da sanyin safiyar ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a hedikwatar ƙaramar hukumar Bunguɗu ta jihar Zamfara, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum ɗaya, yayin da wasu bakwai suka yi awon gaba da su.
Wani mazaunin garin Bunguɗu, Ishaq Bunguɗu ya tabbatarwa da gidan talabijin na Channels faruwar lamarin.
A cewar Bunguɗu, ‘yan bindigar ɗauke da muggan makamai sun mamaye garin da muggan makamai, inda suka riƙa harbe-harbe tare da kashe mutum ɗaya a cikin lamarin.
Bunguɗu ya ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu mutane bakwai da suka haɗa da ɗan Sarkin Bunguɗu Abdulrahman Hassan da kuma tsohon jami’in tsare-tsare na asusun bunƙasa noma na ƙasa (IFAD) Abubakar S/Fada Bunguɗu.
Ya koka da yadda ‘yan bindiga ke kai hare-hare a hedikwatar ƙaramar hukumar, duk da cewa ita ce ƙaramar hukuma mafi kusa da Gusau babban birnin jihar.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 21 a jihar Filato
Bunguɗu ya yi ƙira ga gwamnan jihar, Dauda Lawal da ya naɗa mataimakan tsaro cikin gaggawa.
Ya ce, “Kusan yau da kullum ana kai mana hari, duk da cewa muna kusa da Gusau babban birnin jihar, ba mu san abin da ke faruwa ba, gwamnati ba ta cewa komai, ko da mataimaki na tsaro ba shi da shi tun lokacin da ya ke rantsuwa.
“Ya kamata ya naɗa mai taimaka wa jami’an tsaro domin mutane su san wanda za su ƙira a lokacin wahala, ba mu ma san abin da za mu yi ba a yanzu, ‘yan bindigar za su shiga tsakiyar gari su kashe mutane, abin ya tayar da hankali.
Kun san akwai sansani guda ɗaya da ‘yan fashi suka bi idan kuka wuce unguwar Nahuche zuwa Karakai, suna da wata maɓoya a can kuma jami’an tsaro suna sane da su, ban san dalilin da ya sa ba su tarwatsa wurin ba suka fatattake su.”
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Zamfara, sun kashe mutum ɗaya, sun sace ɗan sarki da wasu mutane shida […]