‘Yan bindiga a Filato sun sace mutum 6

0
30
'Yan bindiga a Filato sun sace mutum 6

‘Yan bindiga a Filato sun sace mutum 6

Aƙalla mutum shida ’yan bindiga suka sace a ƙauyukan Tudunwada da Gyogob, da ke ƙaramar Hukumar Kanam a Jihar Filato.

Sakataren Ƙungiyar Ci gaban Kanam, Shehu Kanam ne, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a ranar Talata.

Ya ce an sace mutanen ne tsakanin ranar Lahadi da Litinin.

A cewarsa, satar mutane ya zama ruwan dare a yankin.

A cewarsa cikin watannin da suka gabata, an yi garkuwa da sama da mutane 30, inda aka biya miliyoyin Naira a matsayin kuɗin fansa.

Abin takaici, mutane biyu sun rasa rayukansu a wasu hare-hare na baya-bayan nan.

Ya bayyana cewa garkuwa da mutane ta yi mummunan tasiri ga al’ummar yankin.

Wasu mazauna yankin sun shiga mawuyacin hali saboda yawan kuɗin da ake biya a matsayin kuɗin fansa, lamarin da ke haifar musu da matsananciyar damuwa.

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro sun kama ;yan bindiga 3 da mai yin safarar makamai

Wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da iyalansu sun ƙaurace wa garuruwansu, gonakinsu, da kasuwancinsu saboda tsoro.

Ƙungiyar ta nuna cewa wasu yankuna kamar Kanam, Gagdi, Gyambar, da Gwamlar sun fi fuskantar barazanar masu garkuwa da mutane.

Shehu ya danganta wannan matsalar da yanayin tsaunuka da yankin yake da shi, wanda yake bai wa mahara damar ɓoyewa da gudanar da ayyukansu ba tare da samun cikas ba.

Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatocin jiha da tarayya da su ƙara inganta tsaro a yankin domin mutane su samu damar ci gaba gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ba.

Leave a Reply