‘Yan bijilante sun kashe matashi a kan bashin dubu bakwai

0
74

A daren lahadin da ta gabata ne wannan bawan Allah mai suna Salisu Abubakar da ke zaune a Shopping Centre, Mararaba dake kan iyakar Jihar Nasarawa da Abuja, ya gamu da ajalin sa ne sakamakon bugu da ƙungiyan mafarauta/ƴan banga suka yi masa bisa ƙara da wani abokin hulɗar sa ya kai musu kan cewa yana bin sa bashi bai biya sa ba.

Bin cikiken labarin ya tabbatar da cewa wannan mamaci ya biya N33,000 daga cikin N40,000 ɗin da ake bin sa wato N7,000 ya rage.

A bokan marigayin su bada shedar cewa ko a ranar Asabar sai da suka gayyace shi ofishin su da ke jikin tsohuwar Mr. Biggs kan titin Keffi zuwa Abuja, inda a nan suka fara begun sa, inda suka sake ƙiran sa a ranar lahadi wanda suka sake bugun sa.

KU KUMA KARANTA:Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe kansa a Borno

A nan ne da suka fahimci sunyi masa lahani, sai suka ɗauke shi zuwa wata Cemist dake tsallake Anguwar Katsinawa inda mai Cemist ya nuna abin ya fi karfin sa sai dai asibiti, bayan da alamu ya nuna cewa ba zai kai labari ba, sai suka yar da shi, suka ranta a na kare.

Leave a Reply