Yadda ɗan shekara 12 yayi garkuwa da ‘yar shekara 3 a Bauchi

1
570

‘Yan sanda a jihar Bauchi sun kama wani yaro dan shekara 12 bisa zargin satar yarinya ‘yar shekara uku.

A sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi Ahmad Wakil ya fitar ranar Asabar, ya bayyana cewa yaron mai shekaru 12 ya yi garkuwa da yarinyar ne a unguwar Magama Gumau da ke karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi.

A cewarsa, wanda ake zargin ya ɗauki yarinyar zuwa wani filin ball inda ya kira mahaifinta a wayar salula inda ya buƙaci ya bashi kuɗi Naira dubu 150, amma mahaifin ya kashe wayar, kafin daga bisani ya yake kiran wanda ake zargin inda ya kira shi da sunansa bayan ya gane muryarsa.

“Bayan wani lokaci, mahaifin yarinyar ya kira wanda ake zargin, ya kira sunansa, amma wanda ake zargin ya yi shiru, ya katse wayar, da gaggawa ya kai yarinyar zuwa gidan iyayenta inda ya shaida wa ‘yan uwa cewa ya gan ta tana kuka a kusa da filin wasan kwallon ƙafa,” in ji mai magana da yawun ‘yan sanda a Bauchi.

Ya ƙara da cewa dangin yarinyar nan take suka kai ƙarar wanda ake zargin ga ‘yan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace.

Wakil ya kuma bayyana cewa yayin da ake yi wa yaron tambayoyi,ya amsa laifinsa kuma ya ce zai yi amfani da kudin fansa ne wajen siyan tufafi da wayoyin salula.

“Bincike ya kuma nuna cewa wanda ake zargin ya sami masaniya ne game da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a lokacin da aka yi garkuwa da abokinsa a jihar Kano.

“Wadanda suka yi garkuwa da abokinsa an biya su kudin fansa kafin a sake shi kuma a haka ne wanda ake zargin ya fahimci cewa dole ne a biya kudi domin a sako wanda aka yi garkuwa da shi,” in ji shi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Aminu Alhassan, ya gargaɗi iyay da su riƙa sanya ido sosai kan ‘ya’yansu.

1 COMMENT

Leave a Reply