Yadda za ka kare shafinka na Facebook da Twitter daga masu ƙwace

5
395

Matakan da mutane yakamata su ɗauka domin kare kansu daga masu yin kutse a shafukan sada zumunta (Hackers).

A wannan lokacin mutane da dama suna fuskantar matsaloli game da yadda ake yi musu kutse a akawun ɗin su irin su facebook, twitter, Instagram da sauransu. Wasu sunanan suna bibiyar yadda za su yi su mallaki wasu bayananka domin su yi maka kutse.

To akwai hanyoyi da dama da za ku iya amfani da su wajen kare kanku daga masu son yi muku kutse. Ga wasu daga cikin hanyoyi biyar da za kuyi amfani da su ku kare kanku kamar haka;

  1. Da farko ka da ku yarda ku saka lambar wayarku ko sunan garin ku ko sunan ƙauyen ku kaɗai a matsayin “Password” a Facebook ko Instagram ko Twitter.
  2. Ka da mutum ya saka “Password” da wani abu da ya shafi bayanansa na shafin facebook.

Misali: Suna na Maryam sai na saka password ɗina a matsayin “MARYAM” ko “MARYAM123” da makamancin wannan.

KU KUMA KARANTA: Anya Facebook dandalin sada zumunta ne kuwa? (I)

  1. Mutum ya saka ” Password” mai wahalar gaske da ya haɗa abubuwa da yawa kamar: Harufa (Alphabets) Babban baƙi (A – Z) da Ƙaramin baƙi (a – z) da Lambobi (0 – 9) da  Symbols (@,#,$,%,-,?,*,£,=) da sauransu. Misali: “Il0v3U_100%@Masoyiyata” = (I Love you 100% Masoyiyata) da sauransu.
  2. Mutum ya yi activating ɗin “Two-factor authentication (2FA)”. Wanda zai taimaka ta yadda babu wanda zai shiga account ɗin ka ko da ya san password da username ɗin ka dole sai yana da “2FA Code” din da aka tura a lambar wayar da aka yi amfani da “Two-factor authentication (2FA)” da shi ko kuma ta cikin manhajar (Authy ko Google Authenticator) da aka seta da shi kafin a iya buɗewa.
  3. Abu na ƙarshe shi ne; a yi activating ɗin “LOGIN ALERT” wanda zai sanar da ku duk lokacin da aka yi ƙoƙarin buɗe shafinku na Facebook da na Instagram da na Twitter ɗin ku. Za’a turo muku da saƙo da cewar “wani mai waya kaza da kaza daga waje kaza ya yi ƙoƙarin buɗe account ɗin ku, shin da izininku ne?” daga nan ko kuce kune ko kuce baku ba ya danganta ga abin da kuke son ku yi a lokacin.

Waɗannan sune kaɗan daga cikin hanyoyi da zamu iya kawo muku su a wannan rubutun da za su taimaka muku wajen kare akawun ɗin ku daga faɗawa hannun masu yin kutse wato Hackers.

5 COMMENTS

Leave a Reply