Wasu da ba a san ko su waye ba da ake zargin ‘yan ƙungiyar asiri ne, sun ƙwaƙule idon wani yaro Almajiri mai suna Najib Hussaini, ɗan shekara 12, a unguwar Kafin-Madaki a karamar hukumar Ganjuwa ta jihar Bauchi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Muhammed Wakil wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Bauchi, ya ce waɗanda ake zargin da suka hau babur ɗin ƙirar Bajaj, sun yi nasarar kama Najib, zuwa wani daji, inda suka cire masa kwallan idonsa da karfin tsiya.
“Najib Hussaini ɗan shekara 12, ɗan asalin jihar Kano, wanda ya ke Almajiranci (karatun Allo) a Kafin-Madaki bai cika shekara ɗaya a jihar ba, lamarin da ya faru a ranar 9 ga watan Disamban 2022, kuma lamarin ya faru ne da shi a Unguwar Yamma, nesa da makarantar allon.
KU KUMA KARANTA:Hukumar ‘yansanda sun cafke mazan da suka yima yarinya fyade, da miƙata ƙungiyar asiri a Ogun
“An bayyana cewa wasu mutane biyu da ba a san ko su waye ba, waɗanda suka zo a kan babur (Bajaj), suka yaudari almajirin zuwa wani gida da ke kusa da su don taimaka musu wajen ƙiran wata mata, inda suka ɗauki Almajirin a kan babur ɗin su, kai tsaye zuwa wani kebaɓɓen wuri kusa da hanyar gona,a ƙauyen, inda suka tsayar da babur ɗin a kusa da wani daji, suka fizge idon Almajirin, da karfin tsiya suka bar shi a cikin jinin.
“Almajirin, ya yi nasarar isa wurin abokan karatunsa, da kuma suka gan shi,sai suka garzaya da shi wurin malaminsu,” inji shi.
Najib ya fito daga Kano kuma ya je Bauchi ne domin samun karatun Al-Kur’ani, a tsangaya, inda ya shafe shekara ɗaya a jihar Bauchi.
Yanzu haka dai ‘yan sanda na neman ‘yan ƙungiyar asirin da suka ƙwaƙule idon Almajirin ruwa a jallo.