Yadda wani mai sana’ar POS ya yi kuskuren cire dubu 100, maimakon cire dubu 10

0
179

shin ya mayar wa mai kuɗin, kuɗinsa?

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wani mai sana’ar POS a garin Potiskum ta jihar Yobe, mai suna Salisu Musa Adamu, ya yi kuskuren cire dubu 100, maimakon naira dubu 10. Yaya aka yi hakan ta faru? Shin ya mayar wa wannan mutumin kuɗinsa? Malam Salisu ya shaida wa wakilinmu yadda abin ya faru kamar haka;

“Suna na Salisu Musa Adamu, ina sana’ar POS ne a nan hanyar Kano dake garin Potiskum jihar Yobe. A wata ranar 17 ga watan Disambar shekarar 2023, wani mutumi ya zo wajena a kan na cire masa kuɗi. Wato zan cire masa Naira dubu 10 ne, sai ladan aiki na (charges) naira 100. Wato zan cire dubu goma da ɗari ɗaya kenan. Sai na yi kuskure na cire naira dubu ɗari da ɗari ɗaya. To shi kuma yana sauri, da na ba shi ‘receipt’ bai duba ba, sai ya yaga, ya tafi. Bayan ya tafi, da na duba kuɗin da nake da shi a cikin ‘POS machine’ ɗin nawa sai na ga ya ƙaru da naira dubu 90.

Shi ne sai na yi ta duba wa a hankali, sai na gano ashe wannan mutumin ne da na yi ‘transaction’ da shi, na yi kuskuren cire dubu 100, maimakon dubu 10. Da na tabbatar a wannan mutumin ne, sai na shiga nemansa. Da farko sai na fara zuwa Banki na shaida musu abin da ya ke faruwa. Na ce su bincika min lambarsa, don a sanar da shi abin da ya faru. Gaskiya hankali na ya tashi matuƙa.

To sai wani maƙwabcina, mai suna Malam Magaji, shi ne mai gidan abinci na Ibrahimawa Restaurant. Sai ya ce min ai yana zuwa wajensu cin abinci. To su ma dai na ba su cigiya, a kan duk ranar da ya zo a ƙira ni. Wani ya ce min yana can unguwar Low-cost. Nan ma kwana na uku ina zuwa nemansa, amma ban same shi ba. A taƙaice dai har zuwa sati uku ban same shi ba. Kwatsam! Watarana da daddare aka ce min an ganshi a wannan Restaurant ɗin na Ibrahimawa ya zo cin abinci.

Sai na ce a gaya masa ga abin da ya faru ranar da ya zo wuri na cire kuɗi, an yi kuskuren cire dubu 100, maimakon dubu 10, don haka akwai ragowar kuɗinsa dubu 90. Ai sai mutumin nan ya ce sam-sam ba shi ba ne. Na ce a gaya masa wallahi shi ne, ya ce sam ba shi ba ne. Na ce a haɗa mu a waya na masa bayanin abin da ya faru. Haka na masa bayanin yadda abin ya faru dalla-dalla, har kalar kayan da ke jikinsa a lokacin da ya zo wajena, sai da na gaya masa. Sai ya ce idan har haka ne, to lallai shi ne. Amma wai yana mamaki.

Sai na ce masa to don Allah gobe da safe ka zo da ATM ɗinka na First Bank, wanda muka cire kuɗin da shi, sai ya ce to. Da ya zo sai muka duba lambobin da ke jikin ‘receipt’ ɗin sun yi daidai da na ATM ɗinsa. Da ya tabbatar da haka, shi ne sai ya ja baya yana ta mamaki. Yana cewa daman akwai sauran irin waɗannan mutanen har yanzu? Lallai ya daɗe yana ta mamakin yadda na yi ta bin hanyoyi daban-daban ina nemansa, don na dawo masa da kuɗinsa.

KU KUMA KARANTA: An kama matashin da ya sace wa mai sana’ar POS dubu ɗari tara a Jigawa

Sai na ce masa wannan kuɗin ai dole na dawo maka da su, saboda ba haƙƙi na ba ne, kuma idan na ci wannan kuɗin, na ci haramun. Kuma tabbas na ci wannan kuɗi, to ruguza min jari na zai yi saboda ba haƙƙi na ba ne. Daman da ban same shi ba, na yanke shawarar zan kai kuɗin banki a ajiye, duk lokacin da Allah ya sa na same shi sai mu je banki a ba shi kuɗinsa. Domin ni ba zan ci gaba da riƙe kuɗi a wuri na ba, saboda kuɗi suna da hau. Kuma sai Allah ya sa na same shi, sai na ji daɗi a raina.

Bayan ya karɓi kuɗinsa, ya ɗauki naira dubu 10 ya ba ni, kuma na masa godiya. Kuma duk lokacin da ya zo wuce wa ta wajena, yana tsayawa mu gaisa”.

El-Mahmud Ibrahim, wanda aka cire masa kuɗi

Wakilinmu ya samu tattauna wa da wanda aka yi kuskuren cire masa kuɗin nasa, mai suna El-Mahmud Ibrahim, ga abin da ya ce “wato na yi mamaki matuƙa ganin yadda wannan bawan Allah ya dawo min da kuɗi na. A kullum ba a rasa mutane masu gaskiya da amana. Wato yadda abin ya faru shi ne, a ranar da na cire kuɗin a wajensa, a ranar na yi tafiya zuwa Maiduguri, sai da na yi sati ɗaya ban dawo ba, kuma wallahi ban ga alert ɗin ba. Kasan wani lokacin Bankuna suna samun matsalar tura alert, kuma ni ban duba balance ba, ballantana na gane abin da ya faru.

Bayan na yi kwanaki bakwai a Maiduguri, na dawo gida, sai na je Ibrahimawa Restaurant cin abinci, ashe ya bar saƙo idan na zo a sanar da shi, yana so zai yi magana da ni. To gaskiya lokacin da ya ke shaida min abin da ya faru, sai na hau musu da shi, har sai da ya ce min na kawo masa ATM ɗina, ya duba lambobin jiki da na receipt ɗin iri ɗaya, sannan na yarda. Lallai wannan ya cika mai gaskiya da amana, Allah ya ƙara masa gaskiya da tsoron Allah. Na ji daɗi sosai gaskiya. Kuma ina ƙira ga masu irin sana’arsa da su yi koyi da shi”.

Bayan da labarin wannan mai sana’ar POS ta karaɗe gari, hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe (SEMA), ta hannun babban sakatarenta, Dakta Goje Mohammed, ta ba shi kyautar naira dubu 50, don farin ciki da yadda ya nuna halin gaskiya.

Leave a Reply