Wani matashi dan shekara 25, mai suna Godsgift Uweghwerhen, yana hannun ‘yan sanda bisa zarginsa da yi wa ‘yarsa mai shekaru uku bulala lamarin da yayi sanadiyar mutuwar ta,
Lamarin ya faru ne a yankin Aladja da ke ƙaramar hukumar Udu a jihar Delta.
Rahotanni sun bayyana cewa,wanda ake zargin ya zane ƙaramar yarinyar ne wacce aka ce ta daɗe tana jinya da, bulalan da yayi mata ya ji mata rauni a jiki.
Wanda ake zargin ya aikata wannan mugun aiki ne a ranar Laraba bayan da yarinyar ta shiga gidan makwabcinsa.
KU KUMA KARANTA:Ɓarawon da kotu ta ɗaure saboda sata ya kuma yin sata jim kaɗan bayan da aka sako shi
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, ya gudu daga wurin da lamarin ya faru nan take da ya lura cewa yarinyar ta mutu sakamakon dukan da yayi mata ba tare da tausayin ta ba.
Dubun shi ta cika ne inda aka same shi a unguwar Ubogo da ke kusa da Aladja yayin da tawagar ‘yan banga da ke yankin suka kama shi tare da mika shi ga jami’an ‘yan sandan reshen Ovwian/Aladja.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin.