An gano gawarwakin mutum shida, ‘yan uwan juna da sanyin safiyar Juma’a da ake zargin tsaka ce ta sanya guba a abincinsu.
Waɗanda suka mutun, sun hada da Mista Adeleke John Samuel, mai shekaru 55, da matarsa, Mrs Pamela Adeleke, mai shekaru 50, da ‘ya’yansu biyu da wasu ‘yan uwansu su biyu.
Wata majiya da ta shaida cewa, an gano faruwar lamarin ne, lokacin da mai gadin gidansu, Mista Lawal Ojo, ya ankare da wani irin shiru da tsakar rana, abun da ba a saba gani ba.
Mai gadin ya sanar da maƙwabta waɗanda suka kutsa cikin gidan sai kawai suka ga gawarwakin mutanen a cikin gidan a dakuna daban-daban.
Dukkansu suna cikin yanayin barci, inji majiyar, wanda ke nuni da cewa watakila sun mutu ne a cikin barcinsu.
A cewar wata shaidar gani da ido, Misis Ifenatuora Ijeoma, mai yiwuwa sun ci gubar ne a lokacin liyafar cin abincin da dare.
Ta sake nanata cewa, bayan da aka duba kayan dafa abinci, an gano wata matacciyar tsaka a cikin tukunyar miya da daya daga cikin makwabtan suka yi, don haka suka yi imanin cewa dangin sun mutu ne daga gubar na tsakar.
Tsaka, a kimiyance aka sani da Hemidactylus frenatus, ƙaramar ƙadangare ce mai santsi, mai laushin fata, ta fito ne daga Kudu maso Gabashin Asiya, amma yanzu ana samunta a duk faɗin duniya.
Tsawon tsaka na kaiwa 15cm, kuma yawanci launin toka ne ko launin ruwan kasa mai haske zuwa launin ruwan hoda.
Yawancin lokaci ana danganta tsaka da gubar abinci mai kisa.
KU KUMA KARANTA:Kano Pillars na jimamin mutuwar tsohon ɗan wasanta ƙofarmata
A cewar wani likita wanda kawai ya bayyana kansa a matsayin Dokta Omotosho, masanin ilimin halitta, “Tsaka galibi ba su da illa, sai dai tana ɗauke da kwayoyin cuta da dama a bakinta, waɗanda ke haifar da babbar illa idan mutane suka ci ko suka sha a ruwa.
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan sanda sun shiga cikin lamarin, duk da dai har yanzu ana hasashen tushen mutuwar iyalan su shi da.