Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar ta kashe hatsabibin ɗan bindiga Ali Kachalla da kuma ƙanin jagoran ’yan bindiga Dogo Gide.
Ali Kachalla da ƙaninsa mai suna Danlami da kanen da Dogo Gide mai suna Machika, wanda ke haɗa musu bom, sun gamu da ajalinsa ne a luguden wuta da jiragen soji suka yi musu a Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja.
“Hare-haren da jiragen soji suka kai sun kashe ’yan bindiga kimanin 38, aka tsare wasu 159,” kamar yadda kakakin Hedikwatar Tsaro Manjo-Janar Edward Bubba ya sanar.
Ali Kachalla shi ne ɗan bindigar da ya yi garkuwa da ɗalibai Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, kuma har yanzu sauran ɗaliban na hannunsa.
KU KUMA KARANTA: Hezbollah ta ce ta halaka sojojin Isra’ila da dama a wani hari kan sansaninsu
Hedikwatar Tsaro ta sanar cewa wani hatsabiban masu garkuwa da mutane da harin ta’addanci masu suna Haro da Ɗan Muhammad suna cikin ’yan bindiga da sojojin suka hallaka.
Sojoji sun tabbatar da labarin ne bayan da farko Aminiya ta ruwaito hakan.
A ganawarsa da manema labarai, Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa ya shaida wa wakilinmu cewa makusantan Ali Kachalla sun tabbatar cewa hari soji ya kashe shi, amma rundunar tana kokarin ta tabbatar.
Bayan ganawar ce Kakin Rundunar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya fitar da sanarwar tabbatar da kashe Ali Kachalla da wasu ’yan bindiga 38.
Edward Bubba ya ce, “a cikin makon nan ne aka kashe kwamandojin ’yan bindigar da yaransu 38.
Edward Bubba ya kara da cewa sojojin sun kuma cafke kwamandan reshen soji na ƙungiyar IPOB (ESN) mai suna Uchechukwu Akpa.
Ya ce an cafke Kapa ne tare da wasu ƙananan kwamandojinsa uku, Udoka Anthony Ude, Ikechukwu Ulanta, and Ezennaya Udeigewere.