Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi ya doke ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Legas, mahaifar Tinubu wato Legas.
Duk da cewa Tinubu ya samu yawan ƙananan hukumomi, Obi ya doke shi da mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
An bayyana dukkan sakamakon ƙananan hukumomi 20. Tinubu ya samu nasara a 11 yayin da Obi ya samu nasara a kananan hukumomi tara.
Ƙananan hukumomin da Tinubu ya lashe sun hada da Agege, Apapa, Badagry, Epe, Ibeju-Lekki, Ifako-Ijaiye, Ikorodu, Lagos Island, Lagos Mainland, Surulere da Mushin.
KU KUMA KARANTA: Atiku ya doke Tinubu a Katsina, jihar Buhari
A ɗaya ɓangaren kuma Obi ya lashe Eti-Osa da Amuwo Odofin da Ikeja da Ajeromi-Ifelodun da Kosofe da Oshodi-Isolo da Alimosho da Ojo da kuma Somolu.
Da aka bayyana sakamakon zaɓen, Obi ya samu ƙuri’u 582,454 yayin da Tinubu ya samu ƙuri’u 572,606. Ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, ya zo na uku da kuri’u 75,750.
Jami’in kula da zaɓen na jihar Farfesa Adenike Oladiji ne ya sanar da sakamakon.
Cikakkun sakamakon:
Jimlar yawan masu zaɓe – 6,942,885
Masu kaɗa ƙuri’a – 1,347,152
APC- 572,606
APGA -2,316
LP – 582,454
NNPP -8,442
PDP- 75,750
Ƙuri’un da aka ƙi – 64,278
Jimlar Ingantattun Kuri’u – 1,271,451 Jimlar Ƙuri’u – 1,335,729
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda Peter Obi ya doke Tinubu a Legas […]
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda Peter Obi ya doke Tinubu a Legas […]