Connect with us

Al'ajabi

Yadda mahaifiyar ‘ya’ya 9 ta rataye kanta a Borno

Published

on

Wata mata mai ‘ya’ya tara mai suna Maimuna ta kashe kanta a unguwar Sajeri da ke yankin Gomari a ƙaramar hukumar Jere a jihar Borno, lamarin ya faru da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, Baa Modu, ya ce yaran marigayiyar ne suka sanar da su cewa mahaifiyarsu ta rataye kanta.

Ya ce lokacin da suka shiga, ɗanta na farko ya yi nasarar yanke igiyar, kuma gawar ta faɗi kasa, a gefenta akwai jaririnta mai watanni 4.

Ya ƙara da cewa babu wata takarda da marigayiyar ta bari kuma yaran sun ce ba su da masaniya a kan dalilinta na kashe kanta, sai dai wata majiya wacce ke kusa da dangin ta shaida cewa ta fara wani abin ban mamaki bayan danginta sun koma gidan da ba ta so.

KU KUMA KARANTA:An ceto ɗalibar da tayi yunƙurin kashe kanta

“Ɗaya daga cikin ‘ya’yanta ya ce mahaifiyar bata son komawarsu gidan bayan an kore su daga tsohon gidansu da ke Bulunkutu Kasuwa.

“A ƙin amincewar ta, marigayiyar a fusace ta tattara kayanta zuwa gidan iyayenta, amma an dawo da ita jiya, ba tare da sanin cewa ta shirya kashe kanta da yammacin yau ba,” in ji shi.

Yunƙurin jin ta bakin ‘yan sanda ya ci tura saboda jami’in hulɗa da jama’a, Muhammad Shatambay, bai ɗauki waya ko amsa sakonni ba.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Matashi ya rataye kansa a jihar Jigawa | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Al'ajabi

An ƙona mutane suna Sallar Asuba a masallaci a Kano

Published

on

An ƙona mutane suna Sallar Asuba a masallaci a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta yayin da mutane ke Sallar Asuba ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Gadan da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a jihar ta Kano, da misalin karfe 5:20 lokacin da ake sallah, a cewar sanarwa ‘yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa da TRT Afrika Hausa faruwar lamarin da kama mutumin da ake zargi, sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Abdullahi Kiyawa ya ce bincike ya nuna cewa mutumin da ake zargi da cinna wutar Shafi’u Abubakar mai kimanin shekaru 38 ya jefa wata roba ne ɗauke da fetur cikin masallacin, sannan ya cinna wuta.

KU KUMA KARANTA: Mahara a Anambara sun ƙona fadar babban Basarake ƙurmus

Kakakin ‘yan sandan ya ce mutum 24 ne suka ƙone a masallacin, da suka haɗar da manya 20, yara huɗu.

An garzaya da duka waɗanda suka jikkata zuwa asibiti don ba su kulawa, amma babu wanda ya mutu a haɗarin, a cewar sanarwar ‘yan sandan.

Continue Reading

Al'ajabi

An tsinci gawar wata ɗaliba a cikin ɗaki a Kano

Published

on

An tsinci gawar wata ɗaliba mai suna Aisha Yahaya ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil, a wani gida da ke wajen jami’ar.

Aisha, ɗaliba ce da ke matakin karatu na uku wato ‘level 300’ a sashen nazarin Kimiyya da Fasahar Abinci na jami’ar wadda aka tsinci gawarta bayan ta koma ɗakinta.

An ce ɗalibar ta rubuta jarrabawarta ta farko a zangon karatun na farko da ake yi a jami’ar.

Wasu daga cikin abokan karatunta sun danganta mutuwarta da shiga cikin matsi da damuwa a dalilin karatu da kuma zana jarrabawar.

A cikin wasiƙar ta’aziyyar, hukumar jami’ar ta bayyana matuƙar baƙin cikinta dangane da rasuwar Aisha Yahaya.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar wani mutum a kan titi a Kano

Sanarwar ta ce, “Aisha ɗaliba ce mai hazaƙa wadda ta rasu a dalilin bugun zuciya. Za a riƙa tunawa da ita a kan sha’awarta na karatu da jajircewarta kan harkokin karatunta.”

Jami’ar ta ƙara da cewa, ba a iya gano wata da ke tattare da ita ba gabanin mutuwarta saboda ba ta nuna alamun rashin lafiya ko fama da wata cuta ba.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like