Yadda mace ta tono gawar tsohon mijinta, tayi faɗa da ɗanta kan dukiyar gado

0
442

Wani ɗan kasuwa, mai suna Dapo Olofinmakin, ya zargi mahaifiyarsa, Olufunmilayo, da tono gawar mahaifinsa, Segun, a yunkurinta na sayar da ƙadarorinsa da ke kan titin Sanya a unguwar Aguda a jihar Legas, inda aka binne mahaifin nasa.

Rahotanni sun nuna cewa Dapo, mai shekaru 47, ya ƙi amincewa da shirin da mahaifiyarsa ta yi na a ɗauke gawar mahaifinsa zuwa wani wuri domin saukaka siyar da gidan da aka binne shi ciki.

Dapo ya yi zargin cewa mahaifiyarsa ta haɗa kai da ’yan sanda daga rundunar ‘yan sanda ta zone 2, Onikan, domin kama shi a gidan mahaifinsa.

Ya ƙara da cewa, ‘yan sandan da suka kama shi da ɗiyarsa da misalin ƙarfe 7:30 na safiyar ranar 30 ga Oktoba, 2021, sun tsare su na tsawon sa’o’i 13, inda ya ƙara da cewa da suka koma gida, sun tarar an tone gawar mahaifin na shi, an ɗauke ta daga inda take.

Ya ce, “Ni kaɗai ne da mahaifiyata da mahaifina suka haifa; A wani lokaci tsakanin 1982 zuwa 1995, mahaifina ba ya kusa don sarrafa dukiyarsa saboda yana da wasu ƙalubale, acikin wannan lokaci, mahaifiyata ta auri wani Alhaji Onisemo, wanda yanzu ya rasu, ta haifi ’yar uwata, Bukola.

“Ina Afirka ta kudu lokacin da mahaifina ya mutu kuma ba zai iya komawa gida don binne shi ba saboda hana tafiye-tafiye da cutar ta COVID-19 ta haifar, don haka, kawuna, Olu Akomolafe, wanda yayan mahaifiyata ne, kuma ’yan ƙungiyar masu gidaje a unguwar Sanya ne suka binne mahaifina.

“Lokacin da na dawo daga Afirka ta kudu, mahaifiyata ta fara ikirarin cewa ta mallaki gidan mahaifina. A yayin da ni da mahaifiyata da wani ɗan uwa muka yi saɓani game da ikirarin kadarorin, a ranar 28 ga Oktoba, 2021, ta zo da ’yan sanda da misalin ƙarfe 7.30 na safe don su kama ni a gidan mahaifina.

KU KUMA KARANTA:An gano gawarwarkin ma’auratan aka sace watanni biyu bayan an biya N7.5 kuɗin fansarsu

“Sun kai ni ofishin ‘yan sanda na Zone 2, Onikan, inda aka tsare ni har sai da suka fito da gawar mahaifina a ranar. Daga baya aka sake ni da misalin karfe 8 na dare.

” Yanzu haka ban san inda ta binne gawar mahaifina ba ko kuma abin da ta yi da gawar, ta yi duk waɗannan abubuwa ne don tana so ta sayar da gidan, ni kuwa na ƙi.” in ji shi.

Dapo ya bayyana cewa wasu masu haya a gidan sun ga mahaifiyarsa ta cire gawar daga cikin kabarin.

Ɗan asalin jihar Ondo, wanda ya jaddada cewa mahaifiyarsa tana neman gidan mahaifinsa duk da cewa ta bar shi da daɗewa kuma ta sake yin aure, ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da su sa baki a lamarin.

Da aka tuntubi domin jin martani, Olufunmilayo, wadda ta dage cewa ta gina gidan.

“Wannan yaron maƙaryaci ne. Na gina wannan gidan kuma yana nan yana yin ikirarin abin da ba nasa ba” in ji ta.

Kawun Dapo, Olu, wanda ɗan uwa ne ga Olufunmilayo, ya ce mamacin ya mallaki kadarar. Ya ce, “Ni fasto ne kuma ba zan yi karya ba. Marigayi Segun, surukina, ya mallaki wannan gidan bisa doka kuma yanzu na dansa ne.

“Ƙanwata ta bar (Segun) ta sake yin aure a 1982 kuma ta haifi ‘ya’ya da ɗayan kuma lokacin da surukina ya rasu a 2020, ba ta ma halarci jana’izarsa ba.

“Ni da ’yan ƙungiyar masu gidaje a titin Sanya, Aguda, mun binne mahaifin Dapo saboda ba ya kasar lokacin da mahaifinsa ya rasu, na yi mamaki da na ji ’yar uwarsa, ta je ta tono gawarsa tana neman gidan, wanda ba nata ba ne”.

Shi ma shugaban ƙungiyar masu gidajen haya a unguwar Sanya Olu Francis ya ce marigayi Segun ne ya gina kadara.
Ya ce, “Kanin Olufunmilayo, Olu, wanda limamin coci ne, kuma ’yan kungiyarmu, sun binne Segun a gidansa lokacin da ya rasu.

“Na yi mamaki da na ji cewa matar ta tono gawar tana neman gidan Dapo ne kadai yaron da mutumin (Segun) ya haifa kafin ya rasu.”

Makin gidan, Wale Ojeyemi, ya ce yana da ɗaya daga cikin takardun gidan, inda ya ƙara da cewa da sunan mahaifin Dapo ne.

Da aka tuntuɓi jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan shiyyar, DSP Hauwa Idris domin jin ta bakinta, ta ce ba za ta iya mayar da martani ba har sai ta duba bayanan.

Ta ce, “Babu wani martani da ‘yan sanda suka yi game da wannan batu har sai na sami cikakken bayani game da lamarin.”

Leave a Reply