Yadda gobara ta ƙone shaguna 19 da masallaci a Kano

0
412

Wata gobara da ta tashi a safiyar
laraba ta lalata shaguna 19 da wani masallaci a kasuwar Rimi da ke karamar hukumar birnin Kano a jihar Kano.

Gobarar da aka ce ta tashi da misalin ƙarfe 1.46 na safe an ce ta yi ɓarna ta kuma lalata kayayyaki na miliyoyin naira.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1:46 na dare daga wani Ahmad Tijjani cewa gobara ta tashi a kasuwar.

Ya bayyana cewa jami’an kashe gobara daga babban ofishin kashe gobara na Kano da Sakatariyar Audu Bako sun yi nasarar kashe gobarar “A yau Laraba, 8 ga Maris, 2023, mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1.46 na safe daga wani Ahmad Tijjani, inda ya ba da rahoton ɓarkewar gobara a kasuwar Rimi da ke Kano Municipal.

KU KUMA KARANTA: Yadda gobara ta yi ɓarna a ƙauyukan Jigawa

“Bayan rahoton an tattara jami’an kashe gobara da ke aikin gaggawa daga cibiyar kashe gobara ta tsakiya da Audu Bako. “Sun (’yan kwana-kwana) sun gano cewa kimanin shaguna 14 na dindindin, wani masallaci da shaguna na wucin gadi biyar ne suka kone kurmus. Wurin da gobarar ta taso ya kai kimanin 75 X 50 ft da ake amfani da shi a matsayin shagunan Kasuwar Rimi,” inji shi.

Abdullahi ya lura cewa ba a sami rahoton wani rauni ko mace-mace a lokacin da lamarin ya abku ba, ya ce an fara binciken ne domin bankado sirrin da ke tattare da wannan bala’in.

Leave a Reply